TA FARU TA QARE.......

Bismillahir-rahmanir-raheem

HISHAAM✍️

Tun jiya da shukra ta bude idonta taga Hanaan take ta ruwan bala'i acikin gidan nan na rasa na meye inda haquri na danake tunanin inada shi ya fara qarewa

Duk yanda  naso abin nan yayi sauqi qin yiwuwa yayi harna gaji na qyaleta

Yau kuwa cikin farinciki na tashi kasancewar Hanaan d'ina ta dawo gida dukda bama da'di da ita

Ta dakinta na shiga abin mamaki bata dakin a tsorace naje qofar toilet sai najita tana wanka banyi auneba naji tana qoqarin fitowa Walk in closet d'inta na shiga na b'uya ina wa kaina dariyan na koma yaro nima kamar ta

Sam bataji motsi naba da confidence d'inta ta shiga d'auko kaya na fara mata tafiyar tsutsa da gan-gan abu taji yana binta ta tsakiyar bayanta suma ne kawai batai ba sbd tsananin tsoro a gurin a hankali na juyo da ita kallo d'aya tai min muna had'a ido ta faara ja da saibaya na fara biyota kamar wanda magnet yake ja cikin idonta nake kallo yadda takanyi qarara naga tsoro acikinsu

Da bango taji ta ha'du cak ta tsaya a hankali na qarasa inda ta maqale matseta nayi a jikin bangon na ha'da qirjin mu a hankali na kuma kafeta da idanu na irin nata har sai da ta gaji da tsaiwa tsakanin hannaye na sai kawai ta sulale qasa ta tsugunna na bita qasan

"You're looking.... sexy"

Harara ta watsa min gashinta dake jiqe na fara sansanawa hakan yana matuqar min da'di kunya ta kama ji ta ko'ina tana neman gurin gudu ganin rigar wanka ka'dai ke jikinta kiss na manna mata a wuya nan take na gane ba ni ka'dai nake hauka na ba ko yaya inada gurbi  kuka  ta fara a hankali har Inajin ajiyar zuciyar ta a fili

"Na tsaneka yadda kake min kamar toy why? Why don't you go to your wife and leave me alone i'm fed up of this?"

"Nasan abinda kake so"

Me nake so, uhm?? faɗamin

Bani kakeso ba kamar yadda ka fada kuma abinda kakeso kariga ka samu gurin wata don haka ni kuma bazan taba baka ba saidai Wanda na adana sbd shi kawai

✍️✍️✍️
Bango ya doka da fist ɗin sa har taji tsoro yace karki qara cewa wani a gabana

Shigewa tayi ta rabu dashi bayan ta shirya tsaf, haushi ya isheta ganin har yanzu tana jin sonsa a zuciyar to gara yau ayita ta ƙare kawai gara yau tayi abinda zasu rabu kwata-kwata .

Bari inje gaban matar sa ince ya sake ni inyaso ta tunzura shi ya aikata hakan, bazan cigaba da zama ba wataran ya yaudare ni ya kaini ya baro ni. Yane kaina nayi na fita ina addu'a sbd yadda gabana ke tsananin faɗuwa ban taɓa zuwa sashen ta ba tun zuwa na gidan saɓanin ita data maida shi kamar bangaren ta

A hankali nake tafiya cikin sanɗa har cikin falon ta ko ina kaca-kaca sai wani wari ke tashi kamar babu helper a gidan kujera na nema na kame ƙafa ta ɗaya kan ɗaya ina jiran ta inda zasu ɓullo Hisham ne ya shigo amma daga gefen sa take a zaune tana shirin magana zata miƙe taga ya wuce fuuuuu be kula da ita a wajen ba da alamu ransa a ɓace yake, niyya tayi ta tafi sai kuma wata zuciyar tace shiga ɗakin idan suka ganki ransu yafi ɓaci sosai.

Cikin ɗakin ta nufa kanta tsaye tana saka kai abinda ta gani yasa ta yi baya da faɗin a'uzubillahi a hankali haɗe da safa ƙirji har ta juya jin maganar sa a ɗakin yasa ta dakata

********************

Duk abinda ya faru tsakanin Hishaam da Hanaan ashe a idon shukra da sauri ta koma part d'inta waya tayi masa tana son ganinsa ji take kamar kafin yazo ta mutu sbd baqinciki, tana zagaye a d'akin tare da kaiwa da komowa sbd ya daɗe be zo ba gashi ana son raina mata hankali injita, wata idea ce tazo mata indaa  take ta cire kayan jikinta tsaf sai pant and bra kawai ta koma kan gado daga gefe ta kwanta akan bayanta tana nishi sama-sama

Ba'afi minti biyuba sai gashi ya shigo cikin cin mur inda ya matsa gefe ya fara latsa wayar sa, lokacin daya lura da ita dan tsorata yayi ya ja da baya sai kuma ya hade rai da fadin meye hakan Shukra??

Hanaan na tsaye tana jin da ganin ikon Allah

"Banida lafiya" ta faɗa da shagwaɓa

Gefenta yaje ya d'osana kadan ya zauna maimakon ya fara dubata sai yace "meke damunki hakan last time I checked you are perfectly alright so what happened all of sudden???

Da sauri shukra ta rungumeshi ganin haka yasa Hanan juya bayan ta da sauri tare da jin wani zafi a cikin ƙirjin ta

Ba kaine ba, ai duk kai ka jawo rashin lafiyar nan ta fad'a da shagwa6a wata y'ar dariya yayi tareda ture ta ya mike ta lura babu wani reaction a taredashi ko kadan saurin miqewa tayi ta riqo collar rigarsa da ƙarfi har button ɗinsa guda ɗaya ya cire da nufin tayi kissing dinshi ya kautadda kansa gefe ta juya daya barin ya juyar dakansa nanma ya matsa baya hadeda cewa please don't ,I'm sick.

Flower vase din dake gurin ta d'auka tayi jifa dashi jikin mudubinta ya fashe yafasa mudubin

Tsorata Hanan tayi ta juyo da sauri

Magana ta fara a fusace

"To hell with your sickness Hisham na dade da gane qaryar rashin lafiyarka amma ganin yadda ka zauna da Hanaan yasa nayi zargin ko maybe you are a gay or something  kai baka sha'awar mace ne kwata-kwata amma sai gashi yau na kama ka kana kyarkyara akan
qaramar yarinya, kamar zaka shid'e a gabana me ta fini dashi?har kana kishi a kanta kamar zaka hadiye zuciyarka sbd  tace wani a gabanka"

"Ko bata fiki ba dai ita matata ce so please don't compare yourself with her"

"Nifa?"

"Ke babu aure tsakanina dake"

Kansa tayo kamar mara hankali tace mekake nufi? cikin kallon tsana ya dube ta  yace

"Na dad'e ina mamakin abinda yasa mahaifinki ya canza shawarar sa akan bani aurenki mutumin dake zargin ni lalatacce ne abin takaici sai bayan aurenmu bincike na ya nunamin ashe sai a lokacin ya tabbatar da kin dad'e da bata tarbiyyar daya baki shiyasa ya neme ni ya nanamin ke, amma abinda yasa banyi komai ba sbd sab'awa maganar mahaifina da nayi akanki nasan hakan zata iya faruwa Allah zai iya jarraba ni akan hakan

Abu na biyu kuma ranar da za'a kawoki gidannan naji hirarku da babbar qawarki hadiza yadda kuka karɓo magani kuka bani na kawowa Hanan shi da hannu na kuka so cutar da matata kikaso ki qara cutarda ita da yadda kikaso rabamu abinda ya hana ni rabuwa dake kenan don inyi amfani dake har ingane kishina i idon matar danake so kuma hakan yayi amfani tunda yanzu tana iya kishi a kaina tana damuwa dani

Duk abinda Hisham keyi Hanan binsa kawai take da kallo ya koma wani mutun na daban yau ɗin a idanun ta

"Nikuma tawa soyayyar fa"?

"Wato shukra bayan na fara son Hanaan saina fuskanci keda bama sonki nakeba kwata-kwata, kawai halayen da kika aro ne kika yaudareni dasu sbd na dolantawa kaina danayi saimai wannan halin nakeso sai gashi ashe kura kika lullub'e da fatar akuya abinda nake hange akanki Allah ya bani fiyema dashi ina neman inyiwa kaina sakaci da rashin hankali sbd makirci da kaidi na mace irin ki

Hakan ya saukar da farin ciki a suk ilahirin jikin Hanan. Ya cigaba

Kuma sanin kanki ne ko a addini babu aure tsakanin mara lafiya dame lafiya,babu kuma aure da zargi, sannan babu aure tsakanin mutumin da yake qyamar haram irin Hisham ya nuna kansa, da kuma macen data riga ta haike wa haram irin ki Shukra inda anan kuma ya nuna ta wannan karon a tsorace shukra take kallon sa yace eh gwajin da kika hana ya fito kafin auren mu wanda kika had'a baki da kwartonki idris kuka b'oye naje na qwaquloshi a inda kuka boyeshi keda dadironki na kuma gane kina dauke da HIV ko a ruwa kika sha ta"????

Koda yazo nan tsorata Hanan tayi inda tayi baya ta jingina bayanta jikin bango gabanta na faɗuwa ta matsa daga saitin ƙofar gabaɗaya tareda dafe ƙirjin ta da hannu ɗaya ta kuma rufe bakin ta da ɗayan hannun tunani iri-iri yana yawo a kanta

"Ta yaya? Ta yaya zakimin haka shukra? me nayi miki? daman wanda yace yana sonka ya tab'a zama maqiyin ka? Dukkan wannan lokacin da mukayi a tare kenan daman bashida wani muhimmanci a gurinki, Shukra kinsan ke din kin riga kin lalata rayuwarki then why! meyasa zakiyi approaching d'ina tun farko?,  why??"

"Kuma badan Allah yasa naji hirarku da babbar qawarki Hadiza ba da tuni na saki jikina dake dukda bana jin wani sha'awar yin hakan amma nasan zan iya biye miki da sunan sauke haqqin ki a kaina kuma har gara ki gogamin cuta akan kisa in rabu da Hanan don rabuwa da ita mutuwar tsaye  ce a gareni kuma koda banaso dole inyi hakan sbd bazan tab'a iya goga mata cuta ba don ni ba macuci bane irinki.

Ai sulalewa Hanan tayi ta zauna a nan sbd ya bata tausayi

To  amma addu'a da rashin alhakinki saiya tonaki na dad'e da furta miki kalmar saki a zuciyata amma bansan me zan gayawa Abba na ba akanki inajin kunyarsa don babu irin gaskiyar da be fad'amin ba a kanki naqi ji shiyasa na kasa rabuwa dake

Shukra! na sakeki saki daya

Faduwa tayi a qasa kamar me shirin hawa bori tace daman zaka iyayi min rashin mutunci haka? duk da'dewar da mukayi a tare?

"Inhar kin kira wannan da rashin mutunci bansan me kike so ba kuma game dani bazan yi miki mummunar addu'ah ba haqqin Allah kawai da kika shiga zai zamar miki darasi komai kuma da kukayi na makirci ya zama alkhairi babban alkhairin kuwa shine aure na da Hanan da kuka zama sila.

Tashi Hanan tayi da mugun sauri ta fice sbd ta fara tsorata kuma da al'amuran

Wlh Hishaam inhar ban sameka ba to saidai kowa ta haqura sbd na riga kowacce mace sonka a duniya kuma na dad'e da gajiya da yadda nake b'oye halayena na asali duk kawai sbd in faranta maka, duk dan in sameka baka isa ka wulaqantani ba wlh

Kuma a gidanka zanyi iddah babu inda zani kafadarsa ya d'aga alamun be damuba ya qara da cewa kome zakiyi nagama zama dake iddar ki a gidan nan batada alaqa dani kuma karki qaramin tsirara a gida don babu ɗan iska a fidan nan, kuma naje na rubuta statement a gurin yan sanda idan Idris ya kuskura na ganshi a area r gidana za'a kamamin shi babu shi babu mata ta kuma da zakice ke kika fara so na me kike nufi???

Matan da suke nuna suna sona sunfi dubu kawai dai na zabeki ne sbd gidadanci da rashin sani wanda hausawa ke cewa yafi dare duhu shiyasa kike ganin hakan amma karki qara wannan tunanin a ranki domin ko a yanzun nakeson mace goma wadanda suka fiki komai idan na fita kafin inje asibiti sun biyoni so you better stop deceiving your self" yana zuwa nan ya fice  ya barta anan tana karkarwa kamar me aljanu

Wayarta ta lalubo ta danna kiran Hadiza tace shikenan ya sakeni duk abinda nake ciki ya sani Hadiza asirina ya tonu ya zanyi?idan na koma gida babana kasheni zaiyi daman sbd wannan auren ya d'aga min qafa inban sami Hishaam ba mutuwa zanyi kaf mazan duniyar nan shi ka'dai yayi min komai da komansa zan iya kwanciya da kowanne namiji amma bazan iya auren kowa ba sai shi sbd shi ka'dai ne zan iya nunawa a matsayin miji na  Hadiza kina jina?

Mekike fa'da shukra me ya faru kike sumbatu haka kama tab'abbiya?

Abinda nike fa'da kenan Hisham ya sakeni sbd ya gane komai a kaina"

"To ita miskilar fa"

"Wai akanta yake cewa bema ta'ba sona ba wlh inbe maidani ba to bazata ta'ba samun saba

Qawata ban zugaki ba amma wannan yayi dai dai itama tabar gidan kawai kota halin qaqane ma ehe tunda aka auri uwarta ban kuma yin rayuwa irin ta da me da'di ba.

✍️✍️✍️
Hanaan jikinta a sanyaye take komai sam ta kasa gane kanta ta rasa abinyi ta kasa gaskata abubuwan da kunnuwan ta suka ji mata d'azun kanta take tambaya me ya kaini ma inda suke??? Amma fa koda hakan ta kasance Allah take godewa saidai sam babu laka a tareda ita shi kuma koma meye ai shi ya jawa kansa dama tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa kan doka ai amma ta kasa dena jin tausayin sa da mamakin irin son da yake mata

Kitchen ta shiga don ha'da abinci taji motsi a bayanta da sauri ta juya a firgice abin mamaki Shukra ta gani

Murmushin yaqe tayi cikin tsoro karo na farko da ganin shukra yabata tsoro ko sbd tasan kishin data ci a kanta ne???  dakewa tayi data tuna ita din wacece taga abin da yafi wannan ma razani ai tace qanwata kina buqatar wani abu ne??? wani irin murmushi Shukra tayi daya bayyana jajayen idanuwanta a fili tareda b'oye hannayenta a bayanta Hanaan ta cigaba da abinda take tace da alama rayuwata ta dameki keda mijinki ganin yadda kukemin sunturi a gida kamata yayi yadda ban damu da kuba kuma kuqi damuwa d....................

Katsewa maganar tayi sbd tsananin azabar data ziyarci qwaqwalwar ta sakamakon abu da taji ya soketa a ciki ta gefe, cikin tsananin azaba ta juyo daqyar tareda kallon cikin ta inda wuqar ta fasa ta dafe sbd jinin da ya fara wanke gurin har yanzun tana tsaye tareda kafeta da jajayen idanuwanta Hanan ta dubeta babu jijiyar da bata tashi ba a kanta da idanuwan ta tace

"Why? me....nayi...miki?

Da qarfi Shukra ta kama wuqar ta zare  da fa'din y'ar iska da haka kike yaudarar kowa kina nuna ke baki damuda rayuwar kowaba nan kuwa kinsan me kikeyi ai shima na gaya masa inban sameshiba babu wadda ta isa ta sameshi wallahi, soka mata shukra take qoqarin qara yi inda Hanan ta riqe hannun gam da dayan hannun ta

Shukra batayi wata-wata ba ta turata baya inda tayi baya gabaɗaya kanta ya daki kitchen counter ta fa'di a qasa babu kowanne irin motsi a tare da ita sai jini da yake zuba daga kan nata 

"Irin wannan ranar nake guje miki shiyasa tun farko banso kika shiga gonata ba sbd ni kaina bansan irin abinda zanyi ba yayinda zuciyata ta harzuqa cikin qaraji take duk wadan nan maganganun, sai kuma ta kalli Hanan din dake kwance nan da nan bakinta ya fara rawa ta kai qafarta tana shurin ta da fa'din

Ke! Ke!! Ke!!!! Kardai ta mutu anan jikin shukra yafara rawa kamar sabuwar mahaukaciya

Wuqar take kallo da jinin dake kwarara da wanda Hanaan ta goga mata jinin lokacin data riqe mata hannu  sai a sannan ta fara tunanin abinda ta aikata

*********
Tunda ya fita yana gidan ya Amina babu abinda ya b'oye mata tace boy nifa ban yarda da wata iddah da zatayi a gidanka ba idan kuma ka amince da hakan to wallahi zan d'auko Hanaan ta dawo nan inka sallameta ta koma don ban yarda da itaba kana ganin abinda sukayi mata....... kamar an tsikareshi yaji shigar maganar da shukra ta fadamai ta qarshe ya dubi ya Amina yace ina zuwa

Muqullansa ya zara da gudu fizgi  motar sa cikeda fargabar da besan na meye ba cikin zafin nama aiko be daɗe ba yake ya shiga harabar gidan yana aje motar bangaren Shukra ya nufa amma ga mamakinsa bata nan be damuba harya zauna sai yaji gabansa ya cigabada faduwa

Part d'inta ya nufa yace a ransa nasamu inci abinci don yau inason inyi bacci me dad'i koda ya shiga babu kowa a part d'in abin ya bashi mamaki sbd yadda qauri da hayaki ke fitowa daga kitchen ɗin be taɓa ji ba  hakan yasa ya nufi kitchen da sauri a bakin qofar  kitchen din yayi kacib'us da shukra cikin mamaki ya fara kallon ta

"Jini....."

Ya fada afili ba tareda yasan maganar ta fito ba sam be tab'a kawo wani tunaniba wuqar hannunta ce tafadi qasa

Nan da nan idanunsa suka fara girma suna canza kala da gudu yayi kitchen inda yaga ta fito Hanaan ya tarar kwance cikin jini babu numfashi tareda ita.

Iyakacin qarfinsa yake jijjigata da kiran sunanta amma babu inda yake motsi jikin ta sam ilminsa da likitancin sa shafi d'auke wa yayi Hanan open your eyes please Hanan, abinda yake iya faɗa kenan stay with me stay with me Hanan Hanaan Han..... gas cooker ya fara kashewa sbd baya iya gani sosai sbd hayaqi ya cika gurin gabadaya cak ya dauketa asibitinsu ya kaita inda ganin halinda ya shiga yasa suka hanashi shiga tareda tura Dr Sadiq gurinsa kuka ya fashe dash  Dr Sadiq ya riqeshi kasancewar yau ce rana ta farko daya tab'a ganin abokin nasa a hakan ya fara lallashinsa kamar qaramin yaro

Kuka yake sosai yace Sadiq ta mutu Shukra ce ta kasheta. Bata mutuba she's still breathing insha Allah za'a ceto rayuwarta

Alhamdulillah alhamdulillah Please kuyi duk abinda zakuyi

Mum ya kira a waya yana kuka ya sanar da ita

A cikin abinda befi minti Sha biyarba sai gasu harda ya Amina da Zee da Ni'ima Mom ce ta qaraso da sauri tace Sadiq wai me ke faruwa ne? ta juya gurin Hishaam wanda ya ha'da hannayensa a bakinsa jijiyoyin kansa sun fito gabadaya sai rigar sa datayi kaca-kaca da jini cikin tsoro da tashin hankali fuskarnan tayi jajir sabida tashin hankali kuka yaqara saki maras sauti kamar wani yaro

Ya Amina ta zauna ta riqoshi tana bashi haquri ruwa aka bashi yasha ya fara ajiyar zuciya ya Amina tace yanzu ina shukran? Sai a sa'annan ya tuna da ita da sauri ya tashi yace ina zuwa.

Be jira  y'an sanda ba ya tafi bayan Mom ta sanar dasu sukace zasu sameshi a gidan ya isa ba da'dewa suka qarasa ya nuna musu komai saidai babu shukra babu wuqar data aikata laifin da ita ji yayi bazai iya haqura a nemota ba tare sukaje gidansu ba'a sameta ba nan take akayi awon gaba da mahaifinta gidan Hadiza ya rakasu sukayi sa'a tana nan

Inda suka damqota tanata musun ita babu abinda tayi tareda fad'in bazan tab'a amsa sharrin da kake qoqarin yimin ba wani dansanda ya daka mata tsawa yace keep your mouth shut ya akayi kikasan sharri ya miki akazo tafiya dake bayan babu wanda yace dake komai, kenan akwai lauje cikin nad'i???

Hankalin sa baya wajen su asibitin kawai yake son komawa ya juya kenan sai ya tuna kama yaga wani abu aikuwa yana juyowa yaga jini jikin zanin Dr Hadiza yace

Shukra tana nan gidan idan ma batanan to wannan matar tasan inda take ku kalla nan ku gani

Kafin a tambaye ta ta nuna inda Shukra ta b'uya bayan an qwaqulo ta, ta riqe Hadiza tayi qam tana ki taimakeni harda shawararki a abinda ke faruwa hadawa sukayi da hadizan akace zata amsa wasu tambayoyi

Anzo fita da shukra ta gaban Hishaam rigarsa ta riqo "kana kallon su zasu tafi dani ko"

Mari ya sharara mata tareda kautadda kai don baya iya magana a lokacin Sam.

Ya Allah me ya kaini auren mahaukaciya irin hakan

Lokacin daya koma asibitin Abba yaje da sauri ya qarasa gurin Abba. Abba ya dubeshi yace "Hishaam! ya akayi haka ta faru?" Da mugun sauri ya tsuguna yace

"Abba tsautsayi ne tsautsayi ne Abba"

"Me na fada maka gameda Hanaan lokacin da zaka auri wannan yarinyar maras tarbiyya?"

Ya Amina ce zatayi magana ya daka mata tsawa saida kowa ya tsorata kasancewar Abba baya ta'ba yiwa ya Amina fa'da

Shiru tayi jikinta na rawa cikin tsawa ya cigaba da magana:

"Dan ubanta ya bawa mutum irinka auren yarsa bashi yake nuna baya sonta ba ko kuma shi besan me yakeyi ba fa tsabar yadda ce da ganin nima na isa da ita

Yanzun abokinka ya tabbatar min da cewa Hanaan ko da zata rayu zata iya shiga coma sbd kanta ya bugu sosai to kayi addu'ar kada wani abu ya sameta don idan wani abu ya sameta wallahi nida kaine, kuma daga yau ka gama aurenta ko kana so ko baka so saika saketa qirjinsa ya dafe da yake masa rad'ad'i tareda sulalewa qasa yana hawaye Mum ce tayi kansa don lallashi wata muguwar harara Abba ya watsa mata ta qame a gurin tana kallon Hishaam cikeda tausayin sa, kuka yake sosai harda sauti yana bazan iyaba wlh mutuwa zanyi please Abba ka taimaka min abin zaimin yawa ni'ima ce ta rungumeshi tana lallashinsa sbd itama kukan take yi ya mugun bata tausayi

Team en da suka karbeta ne suka fito bayan awanni hudu cur da sauri suka nufesu kasancewar mahaifinta ya iso tareda Amal da ma'aruf surgeon d'in ya fara magana alhaji an ceto rayuwarta for mow amma babu tabbas d'in lafiyar ta sai a jira farkawarta hanjinta ya fashe sbd wuqar ta shiga amma andinke saidai kanta ya bugu da wani abu me qarfi kuma hakan yafi illa fiye ma da ciwon wuqar dake cikin ta,  kuma jini yadan bazu ka'dan wanda zai iya haddasa matsala sbd (traumatic head injury is one of the most common things) dayake saka mutum shiga coma Hishaam ne ya katseshi da tambaya

"Yanzun me kake nufi"?

Dr Khalil yace baka buqatar qarin bayani sbd kasan me yake faruwa musamman ma dayake b'angarenka ne daga cikinmu babu wanda ya kaika ƙwarewa da experience a nan bangaren sai dai kaqi ganewa da gan-gan ko sbd wani dalili

Amman inason ka tattara duk nutsuwarka kai fatan Allah ya bata lafiya, zubewa ya sake yi tareda cewa

"I can't"

Sam ma'aruf bayajin tausayin sa saima tausayin yar'uwarsa daya sakashi jin haushin Hishaam d'in dake wani nuna ya damu da ita yanzun.

******************
TWO MONTHS LATER
*********************
Kimanin wata biyu kenan babu wani canji gurin Hanaan sai ma ICU da suka maidata wato (intensive Care unit) inda a tsahon wata biyun nan sam Abba ya saka securities da guards ko'ina ya hana abar Hishaam shiga gurinta yace be ma yadda dashi ba yayi naci harya gaji inda hakan be hanashi zuwa kullum ba da tsayuwa bakin qofa

Ya rame gabadaya yayi baqi ya fita hayyacinsa daka ganshi zakaga damuwa qarara ga wata suma ko'ina harya fara samun matsala a gurin aikinsa ginin sabon asibitin da yakeyi ya tsaya cak kullum banda son ganin Hanaan babu abinda yake babu abinda be saqaba sam be zaci ganin Hanaan zai taba yi masa tsada haka ba ga Abba yaqi ya saurareshi daya tunkareshi sai yace ina takardar saki inya kawo sayi magana inda yakan haqura shi kuma

Yakan zauna musamman ya dinga tunanin abubuwan da suka faru na rashin kyautawar sa da kuma juriya da haquri irin na yarinyar tabbas Abban sa yaso shi da babban alkhairi shiyasa inma yaji haushi wani lokacin yake masa uzuri
Hishaam bashida masaniyar meke faruwa katsam Abba ya tura yazo murna ta isheshi yana zaton za'a bashi iznin ganin matarsa ne amma koda yaje Abba na miqewa yayi ya fara magana yana tafiya tareda goya hannayensa a bayansa

"Hishaam yaune insha Allah zan tafida Hanaan qasar waje don nema mata magani zazzaro ido ya fara tareda hade wani bushashshen yawu yace Abba nima zani dan Allah Abba zan iya taimakonta

Hannu ya daga masa da cewa ai duk abinda zakayi ka gama tsaf kuma bama zaka san inda zan kaita ba

Amma ai ya kamata a shawarce ni Abba ai har yanzu matata ce

Lallai kam matarka ce ammafa na zuwa ɗan wani lokaci, tunda kaqi ka saketa inta warke ta nemi hakan da kanta ai kayi ko?

Da rarrafe ya nufi Abba Saida yaje dai dai qafafun sa sannan ya tsaya ya fara magana a hankali "Abba nasan na sab'a maka amma banajin tsanar da kake min takai hakan don girman Allah karka rabani da matata yar'uwata wallahi Abba mutuwa zanyi sam bazan iya rayuwaba itace rayuwar kuma har yanzun nine me matakin farko daya kamata in kula da ita fiye da kowa Please, please and please ka tausaya

Gurin mum ya juya yace please Mum please Mrs Baita ki roqi mijinki duk abinda nayi na laifi wallahi zan gyara kuma na yarda yayimin hukunci amma banda wannan sbd ana magana ne akan rayuwa ta don Allah karya rabamu ki roqe shi mana"

kuka Mom keyi sbd ya gama bata tausayi rungumeshi tayi yana faman sumbatu kamar na goye tana qara qanqame shi sbd tana tunanin ya fara tabuwa tana nadamar rashin tsayuwar ta akan al'amuran sa da Amina take gaya mata da duk hakan bata faruba gashi garin tayiwa y'ar wani mugunta hakan ya qare a kansu ita da danta

Ficewa Abba yayi ya barshi nan yana faman magiya mum cikin jin tausayin sa tace

"Ka sanshi sai dai wata banda Hanaan tunda ya hau dokin zuciya kwallace ta zubo mai ba tareda ya kulaba ya d'aga kai ya kalli mom yace ai wlh daga kan Hanaan har abada na gama aure saidai in bakuda rabon ganin gudan jinina a hankali ya tashi jiki babu kuzari ya nufi dakinsa dan yanzu ya dawo gida tun ranar da abin ya faru sai dai ya raka yansanda amma sam ya daina zuwa gidan

Da yaje gidan saiyaga kamar a ranar ne abin ya faru

Ta qofar baya yaje ya bawa guards d'in asibitin cin hanci don na Abba duk yadda zaiyi sun hanashi yana shiga dakin ya hangota kasancewar ita ka'dai ce dakinta a hankali yake tafiya jikinsa babu inda baya rawa tana kwance idanunta a bude sama take kallo akan gadon ya zauna hannuwanta ya kamo yace

"Hi lazy bones ki tashi mana sai kawai yaji yana son yayi kuka

Cigaba yayi da kukan harya isheshi yace dan Allah Hanaan na tuba ki yafe min haqiqa nayi wasa da rayuwata sbd rayuwarki tawace ina neman gafararki sbd afuwar da kike wa maƙiyanki  ki taimaka kema karki nemi rabuwa dani kamar yadda Abba keso kobaki warkeba inason ki a haka kuma zan iya zama dake inkula dake

Nasan kina jina please kar kiyi fushi dani ki yafe min kinji ko? akan gadon ya kwanta ya d'ora kansa akan qirjinta yana kuka silently

Daga waje ya fara jin hayaniya sam be motsaba sbd jikinsa da yayi laushi. Turus kowa yayi saboda yanayin da suka ganshi Abba ya hade gira yace ka fita anzo tafiya da ita, sai kuma ya fara kuka me sauti tareda qanqameta abokansa Abba yasa aka kira suka shigo Sadiq ya fara bashi haquri yace Sadiq ka taimaka min inajin zuciyata tanamin zafi yace to taso amma ina daqyar suka bambaresa daga jikinta yana kuka kamar qaramin yaro Amal kanta saida ya bata kuka sbd tausayi inda Dr Sadeeq lallashin ya zamar masa biyu.........✍️

Comment and vote please 🙏

Comment