NADAMA

Wasu hawayen yaji suna zuba ya rasa yadda zaisa kansa da tsananin tausayin ta da sabon shauqin sonta kenan a irin wannan rayuwar ta tashi amma kuma tazo tayi rashin sa'ar miji wulaqanci, ko in kula, da kallon banza da d'aukar zuga babu wanda ban mata ba. A haka kenan ta tashi amma take nuna komi ba komi bane gashi Mom bata sonta ko kara basa mata ni'ima ma haka shiyasa take dunbin girmama masoyanta takanyi komi sbd su.

Hannun ta da yake dunqule ya bude qwayoyin bacci ne a ciki ragowar wanda tasha ga ragowar busassun hawayen ta kuka yake mara sauti ya d'aga kanta a hankali ya d'ora akan cinyarsa yana jin sabon sonta yana shigarsa yana shafa gashinta a hankali da fadin forgive me sweet one, forgive me please inda ya lumshe idanun sa hawayen sa na sauka a hankali ya jingina bayan sa da karagar gadon ta

Baze ta'ba yafewa Hadiza da Shukra ba akan abinda suka yi musu dukda cewa wani abin laifin sa ne, kuma Idris saiya gane kurensa shima kuma zai fa'da masa me yasa ya shigar masa gida har d'akin matarsa ta sunnah ya saka masa cameras suka kalle masa mata suka kalle shi a matsayin shashasha kuma wawa gashi kuma sun jefa zargi tsakanin su sa'annan duk wani asiri da yake b'oye saiya tono shi ya kuma godewa Abban sa akan zabin da yayi masa ya kuma yi kaico da irin zabinsa wannan shine Ana zaton wuta a maqera anganta a masaqa kuma zaiga ta yadda zasu rabashi da matar sa da yakejin yafi sonta akan rayuwar sa.

Amman komi zai daidaita zaiyi maganinsu baki daya a nan ya kwana sam bata saniba sbd tasha maganin bacci over gabda asubha ya gudu ya koma d'akinsa gudun karta tashi ta ganshi anan tayi rigima

Yasan yau zasu fara jarrabawa sa'annan baya buqatar su ha'du da Shukra da wuri yayi wanka ya shirya cikin qananan kaya yayi wuf ya shige part d'inta. Lokacin daya shiga tana kan dining ta shirya tsaf cikin uniform dinta tana ganinsa ta ha'da ranta tareda d'auke kai dad'e duniya bata sanshi ba kyau ta masa hakan ya sakashi fara'a babu tsammani can saiga Shukra sam ba zaka ce ba'a tare sukeba haushi ya qara kama Hanaan opposite da ita ya zauna inda beyi auneba saijin Shukra yayi kusa dashi babu wanda ta kula a cikinsu balle fa su sami arziqin gaisuwa Mariya me aikinta ta yiwa magana

Mariya zuba musu abinci mana,ba musu ta hau zuba musu

Harara Shukra ke binsa da ita har Hanaan ta gane tace a ranta ku qarata ita ta fara gama cin abincin ta ta miqe tace to kamar yadda nake tunanin kun sani niba mutum bace me son uninvited guests like you people ba,ta fa'da tana nuna su don haka zaifi kyau ace you both stay within your limits and you don't have to come all the way here to eat you can order and eat at your own area without making anyone worry, anyway. Jakarta ta goya ta dubi Mariya tace in sun gama ki rufemin part d'ina sai dare zan dawo da sauri ya kalleta yace "ina kuma zaki"? ko kallon sa bata yiba ta fice da sauri ya biyota har bakin qofa yace "ki tsaya in kaiki" tace "zan sami lift a hanya yaya ka koma wajen me ɗakin ka"

"me kika ce.....?

Shukra ce ta katseshi ta hanyar riqe masa hannu inda Hanaan tayi saurin ficewa daga gidan tana huci sbd saurin datake don sam ta tsani ganin d'aya daga cikin su ba kuma taso su gane hakan.

Dr.a ina ka kwana?

"A dakin Hanaan mana"

" whaaaat"?

"Yes eh ko akwai matsala da hakan?" "Wannan wane irin cin fuska ne? kwana na ka d'auka ka kaiwa wannan yarinyar? ranar daren farko na.....?

"Ba sunan ta wannan yarinyar ba sunanta Hanaan, ba wannan yarinyar ba bakya ganin batada lafiya?

"Babu ruwana da rashin lafiyarta kai ko d'okina ma baka yi"?

Juyawa yayi ya fuskanceta yace au d'oki ake in anyi aure?

"Eh mana baka sani ba"?

"Ya za'ayi insani"?

"To a gaskiya a qallah saika kwana bakwai a guna kafin ka tafi gurinta tunda nima budurwa ce

"To ai itama haka kuma ita ta fara zuwa kuma babu abinda mukayi tunda tazo abinda na duba kenan"

wannan matsalar ka ce ta fada gamida tafiya ta bashi guri.

Murmushi yayi yace yarinya zaki gane

Yauma da safe babu kunya sai gasu a tare baqincikin Hanaan kasa b'oyewa yayi Hishaam harda wani miqo mata plate wai aishi baqonta ne don haka dole tayi saving dinshi babu musu ta zuba masa duk abinda yake buqata ta zubawa shukra babu wanda ke magana a gurin sai Shukra sai zuba take kasa cin abincin Hanan tayi don takaici don me zasu shigo mata bangarenta idan bazata iya girki ba su nemi cook mana ko su ringa order daga waje ita ba babar kowa bace bafa shiru tayi ta dafe kai cike da takaicin su da alwashin yin maganin su.

Washegari daman da makaranta da wuri ta gama break fast d'inta tana shirin tashi sai gasu ko kunya inda hakan ya saka ta dariya sai bayan sun zauna ta kira Mariya tace "kwashe kayan abincin nan"

"Eye?"

Mariya tace gamida sosa qeya tana kallon Hishaam ta daka mata tsawa tace

"Ki kwashe kayan abincin nan nace ko kece kikayi girkin???"!

A'a Cikin sauri mariya ta fara abinda aka sata jakarta ta goya tana qare musu kallon banza ta fice ta barsu nan.

Maimakon Hisham yaji haushi abin mamaki wai dariya abin ya bashi harda buga ƙafa

Cikin takaici shukra ta dubeshi tace Dr wai meke damunka ne? tunda nazo gidannan duk ka canja min sai kace wani mutum na daban sam banyi tsammanin haka daga gareka ba kodai akwai wata matsala ne?

"Ki tambayi kanki da qawarki Hadiza sbd nima da ban taɓa tsammanin haka ba" ficewa yayi ya bata guri.

Gabad'aya rayuwar Shukra ta gigita sam yanda ta zata ba hakan take ganiba gashi Hanaan yanda take so haka take yi a gidan babu wanda ya isa ya sata ko ya hana ta ita kuwa komai saita tambaya to tafa fara gajiya da irin wadannan abubuwan

A bangaren Hishaam kuwa yana lura da yadda Shukra ke tafiyar da al'amuran ta yasha ban ban dana Hanaan sosai sbd ita batada qyamar hada guri da maza a iyaka saninsa sai Hanaan bata nan ake fitar mata da garbage da sauran ayyukan daya shafi yaran gidan kuma bakin qofa take fito musu da abincin su suje su d'auka amma shukra har falonta take kiransu sannan ga jajibe jajiben qawaye kamar itace yarinyar gashi sam bata iya komai ba a fannin girki a taqaice dai ko ruwan tea ta dafa sai yaji ba da'di irin na sauran mutane zaman jiran lokaci kawai yakeyi da ita sbd ya riga ya tsara dukkan abinda zaiyi baya so selfishness d'insa yayi yawa ne kawai

Yau lahadi tun safe take shiri yana kallon ta a kwance yake tace to Dr nizan fita ya dubeta sheqeqe yace babu inda zaki

"Kaga Dr bazai yiwu bafa ina kallon a gidannan qaramar yarinya tana yadda taga dama dakai sa'annan ni kace zakamin iko baze yiyuba"

"To ai ita bata kiran kanta da sunan matata kefa"?

To inko haka ne saidai ka sake ta yanzun inyaso sai asake sabon zubi ni kuma duk abinda kakeso zan maka idan ma kace daga yanzun kar in sake fita shikkenan"

"To waima ina zaki? ke bakida wata ranar hutu ne a rayuwarki yau dai ba ranar da kike aiki bace ko?"

"Eh amma fitar da zanyi tana da matuqar muhimmanci a gurin mu baki daya sbd magani zan karbo maka"

Da sauri ya juyo ya fuskanceta yace wa zaki karbawa magani?

"Tace kai mana sbd kana buqatarsa idan shashashar yarinyar can zata iya zama dakai a haka toni ba shashasha bace bazan iya ba"

Tana maganar tana girgiza jikinta kalar ta ta asali tana son fitowa

"Au kice zama a haka shashanci ne?"

"Wai Dr dan Allah meye matsalar ka? ace ina waje abin kamar gaske amman daga aurenka komai ya canza lokaci guda?"

Shawarar da zan baki itace karki sake ki bata lokacin ki don inkin karbo ma saidai kisha bana shan abinda ban yarda dashi ba sbd naga illar hakan, to ai dama da niyya kake yi tunda idan magani ne aiba finka sani nayiba

Ficewa tayi ta barshi anan har yamma yana jiranta

Ruwa ake sosai,yana game a wayar sa tun safe yake son yaje wajen ta amma ya kasa ya rasa me yasa kunyar yarinyar yakeji yanzu sbd yacca ubangiji yake nuna masa iyakar sa a kanta jin ya kasa daurewa yasa shi jan ɗan guntun tsaki mtss

Kan sofa ya jefa wayar ta miƙe ya fita, sashen ta ya nufa amma abin mamaki bata nan ranar data jiƙashi ya tuna unexpectedly ya fara murmushi inda ya zagaya wajen wasan ruwan nata, ai kuwa tana can saidai banbanci ɗaya shine yau tana zaune ne kurum a cikin ruwan yana dukanta ta ko'ina tayi shiru bakinta ta rawa sbd sanyin ruwan da isakar da take kaɗawa a gurin

Tsorata ya farayi da yanayin nata da sauri ya ƙarasa ya tara mata lemar wajen kanta jin ruwan ya tsaya ya sakata ɗaga kai don ganin abinda ya tare ruwan batayi ko ƙoƙarin ta kula shi ba inda ruwan ya fara zane shi sbd umbrella ta musu kaɗan ,kusan minti biyar yana tsaye ganin batada kowanne motsi yasashi zama kusa da ita cikin ruwan sai a lokacin ya samu ta kalleshi idanun nan sunyi fari fat.

"Ki tashi daga ruwan nan wanka ya isa haka ko so kike kiyi zazzaɓi "??

Me ya dameka dani? Tayi maganar murya a dashe

"Babu" Ya bata amsa

Please ka tafi ka bani guri ka ƙyaleni haka mana wlh banason ganinka

Har akan halshen sa yaji ɗacin maganar amma saiya haɗiye sbd shiɗin me laifi ne a gareta yasan he deserves it

Amma dae kinsan gaba nake dake ko?? Kuma na isa in faɗa aji

Eh gaba kake dani amma da maganar ka data Chinese duk ɗaya ne a gareni sbd bazan taɓa gane yaren ku ba

"Amma ai zaki gane ta Abba ko? A lokacin dana sanar dashi cewar kinason ki halaka kanki

Kallo na tayi da idanun ta da suka fara zubar da hawaye kuma tace

Sai yaushe zaka barni in huta?? In fita daga cikin jarrabar auren ka daka ruftani a ciki sai yaushe zaka dena yanke hukunci masu zafi a kaina???

Kinga Hanaa...........

Miƙewa tayi ta shige ciki da sauri na tashi na bita a baya sbd yanayin yacca take tafiya kai kace wani robot ne washroom ta shige ta cire komai na jikinta tana fitowa ta watsomin kaya na da na taɓa bari a ƙofar ɗakin ta kallo na bita dashi

Ka kaiwa matarka ta ajiye maka I'm not your wife anymore

Closet ta shige zata canza kaya yace

To ai shikkenan na tafi wajen matata

A ranta tanajin kamar ana watso mata wuta amma a zahiri tana faɗin gara kowa yasan inda ya kama

**********"*"*******

A tsaye yake ta saman barandar sa har ruwan ya ɗauke Hanaan ce ta fara dawowa bayan tayi parking ta debo kayanta niqi niqi daga gani daga shopping ta dawo  au daman fita tayi???yana kallon ta cike da sonta da sha'awar kyawawan halayen ta da dabi'un ta da addinin ta da kyawun ta kai dama komai nata yayiwa kansa hauka dayake zata wai sha'awar ta yakeyi har yake punishing kansa a kanta besan haka so yake ba sai a kanta...

Kamar ance ta d'aga kanta suka ha'da ido tayi masa masifar kyau kasancewar atampa ta saka be saba ganin ta da suba kamar yana danna waya yayi inda yaketa daukanta photo a dukkan movements ɗinta ita kuma tayi tsaki ta cigaba da abinda take yi motar shukra ce ta shigo harabar lokacin Hanaan ta dawo kwasar ragowar kayanta da sauri ya sauko cikin kwarkwasa Shukra ta tafi da sauri ta rungumeshi ba zato shima sai kawai ya rungumeta sbd yanason ganin abinda Hanaan zatayi sbd a duk lokacin data kusanta shi da shukra ta nesantashi da kanta yanajin kamar zai kama da wuta shiyasa zai rama hannuwanta a take suka gaza daukar kayanta suka zube a qasa da sauri Fillo me aikin gidan yayo kan kayan don taimaka mata gabansa ne ya fadi ganin ya doso masa mata ta sunkuya ta fara kwasa inda ya gallawa Fillo harara inda hakan tasa ya koma da sauri ba tare da Hanan ta kula da hakan ba qwalla ce ta digo akan kayan ta kwashe kayanta ta wuce ta barsu a tsaye ba tareda ta ko ƙara kallon inda suke ba.

**************
Daga yau komai yazo qarshe Hishaam insha Allah kaji, idan ka qara ganina a gidan nan kayi min duk abinda ka ga dama, a ranta take wannan maganar

Kwana biyu kenan baya ganinta ko dakin baccinta ya shiga baya ganinta Mariya ya kira ya fara tambayarta tace yallabai nidai ta ha'da kayanta tacemin tayi tafiya tun ranar da suka gama jarrabawa kuma tace kar a nemeta

"Kina nufin Hanaan ta gama makaranta ban sani ba"?

"Eh yallabai don ranar anyi girki me yawa daga gidan ya Amina an tafi dashi makarantar a canma muka wuni ana ta hotuna

Damn it!

Wayarta ya fara kira tana ringing amma babu amsa dakinta ya shiga inda ya tarar da wayar a yashe akan gado dakin babu kowa 72missed calls ya gani ciki na ya amina yafi na kowa yawa na Amal na ya Ma'aruf na Zee saikuma nashi kardai

What..... the..... fuckkk is happening......

Yarinyar nan ta gudu fa gabansa ne yayi mummunar faduwa yau kwana uku kenan daya kula shukra don taji haushi kardai.....? kardai hakan ta ja masa musiba. Fuck me

"Shit!"

Da gudu ya koma dakinta ya rasa ma me yake yi a dakin to wazai tambaya ina take?

Amal  ya faɗa da ƙarfi yawwa Amal abinda ya fara fa'do masa kenan gidan ya nufa Kai tsaye part dinsu yaje yayi sa'a tana nan anan yaga Maryam ya cika da mamakin ganinta a gidan Amal na ganinsa tace muje waje kamar zata rakashi suka fita suna fitowa waje ta hade rai tace ina Hanaan ta tafi?.

Dasauri ya dubeta yace abinda zan tambaya kenan

Kuka ta saka tace to wlh tunwuri ka nemota idan kuma ba haka ba zaka jawa kanka rigimar da bakasan qarshenta ba wlh har gaba da gaban Abba sai munje akan y'ar uwata me haquri da juriya da sanin ya kamata wlh bazaka tab'a samun madadin ta ba a rayuwarka don yanzun babu mata irin su Hanan Ashe ?  Ashe daman so ya taɓa zama laifi???juyawa tayi ta bashi guri batare da ta saurareshi ba.

Ya jima a tsaye maganganun ta suna yawo a kansa sbd yasan dukkan abinda ta fad'a din haka yake to yanzu ya zaiyi?

Daga nan gidan ya Amina ya wuce a bakin qofa ya hadu da Zee Amma saita wuceshi taqi gaidashi mijin ya Amina yana gida bayan sun gaisa dashi falo ya dawo banza ya Amina tayi dashi sai bayan ta gama hirar ta sannan tafito ta same shi.

Wani mugun yawu ya hadiye sbd irin kallon da take masa ya jure yace please please sis find out wherever she is, I'm in total mess

"And why would i do that?"

"Please sist......

"Dakata BOY nagaji da yadda Mom ke goyon bayanka wallahi na baka kwana biyu idan Hanaan bata dawo ba wlh kaida Abba tana magana muryar ta har rawa take fuuu ta tashi ta bashi guri. Hanyar da tabi yake bi da kallo maganarta ta tsorata shi amma yafi jin tsoron halinda Hanan din zata iya shiga fiyeda wanda yake ciki ta 'bata kenan ko me ??ina taje? Su waye akan hanya?  Ina ta sani?? Kuma da wa ta haɗu. Ooh yaa rabb

Abu wasa-wasa yau kwana shidda bata nan gashi gobe ne wa'adin alqawarin ya Amina zai cika yana dakinta kamar kullum littafin ta ya hanga akan mirror ya d'auka yana sansana wa sbd qamshin ta dake manne jikin littafin yana tuna kyakykyawar fuskar ta yana dagawa takarda ta fa'do yayi saurin sunkuya wa ya d'auka ya fara karantawa idan kayi sa'ar samun wannan takardar kuma inka yarda zaka sakeni ka tabbatar da cewa zaka sakeni zan dawo rayuwarka da wannan sharadin ka duba wayata ka kira lambar Hande

Wurgi yayi da takardar daga aljihunsa ya ciri wayar tata ya duba saiga lambar da sauri ya kira daqyar ta shiga harta katse ba'a daukaba ya cigaba da kira har yayi sa'a aka d'auka wake magana

"Hi..... Hishaam ke magana barka da rana ya ƙarasa maganar yana lashe busassun laɓɓan sa ya gama ƙaguwa yaji muryar matar sa yayi missing ɗinta over. Ja'iri bani amsa gaisuwarka saida matarka ta baroka sannan kasan kanada dangi aida na'isa da ita da bata dawowa saita shekara ina bakama san hanyar niger ba? ke Hanaan kizo mijinki ya bugo gabansa ne ya fara faduwa kamar sabon saurayi

Assalamun-alaikum tace maqalewa muryarsa tayi ya lumshe idanunsa yana ganota da kyakykyawar fuskarta tana fara'a jin yayi shiru tace tace hello! a karo na biyu gyaran murya yayi yace hello sweet one Allah yasa kina lafiya?

Qalau dftn ka yarda da abinda na nema? da sauri yace

Indai kika dawo I'll do whatever na yarda zanmiki duk abinda kikeso banda wannan ya qarasa maganar a ciki-ciki tace eye? yace eh na yarda,pink promise qit ta kashe wayar,

Damn! To Niger ina????

Iyaka qarfinsa yake kira amma sam taqi qara shiga kamar yayi jifa da wayar yaji don shi a dangin su ma be tab'a sanin wata wai Hande ba

Yau satinta guda kenan kullum cikin fa'da suke da Shukra a kanta sbd ya fara gigita da rashin ta kusa dashi gashi babu alamunma zata dawo gashi wayar ta daina shiga tun jiya yake kira a banza jifa yayi da wayar tasa cikin qunar rai ba da'dewa ta fara qara da sauri ya d'auka ba tareda duba me kiranba ya Amina ce ke magana cikin rad'a boy kazo ga matarka ta dawo amma karkazo yanzu sbd karta gane nice na......

Da sauri ya fita ya tada motarsa sai gidan da sand'a yake shiga gidan da sallama qasa-qasa lab'ewa yayi ganin ta ta fito daga kitchen riga da wando ne a jikin ta wandon ya kama ta blue ne rigar rose pink armless ce sai top har kusan gwiwarta sai mayafinta dabe rufe dogon gashinta ba kyawunta yake kallo kamar kullum qara halittar ta ake sannan qara girma take surorinta na kyau na qara bayyana tray d'in hannun ta Zee ta karb'a tana ta murna ta jata suka shige d'aki

Table d'in yaje yayi sa'a hot coffee ne a ciki ya d'auka ya fara sha yana tuna irin dad'in abincinta yana shaqar daddad'an qamshinta daya cika ko'ina abinda yafi missing fiye da komai a cikin gidan yana jiyo dariyarsu ita da Zee kasa haquri yayi ya ajiye kofin hannun sa da sauri ya nufi dakin ya bude qofar a tare suka juyo sbd yadda ya bude qofar ganinsa yasa fuskarsu canzawa daga dariya zuwa cin mur cikin dakin ya shige ya fara kafeta da ido Zee ce ta fice da sauri tareda hararar sa bayan Zee tabi da sauri yayi saurin riqota ya dawoda ita

"Hey  sweetie Ina kikaje?

Yayi maganar can qasan maqoshin sa

Ta cije bakinta tace babu ruwanka da inda naje kaidai kawai ka cika sharadin dawowa ta da qarfi ya rungumeta tayi saurin cijewa gudun karsu fa'da kan gadon Zee qin rungumeshi tayi amma saitaji shaqar iska nabata wuya sabida damqar datasha tureshi tafara yi tana gyara gashinta daya manne ajikinsa ba zato ya manna mata d'an gajeren kiss a lebenta ta wawwaro ido a tsorace cikin takaici tana goge gurin da bayan hannun ta

Har yanzun kina sona tunda kika kasa bari in hadu da fushin Abba na don nasan abinda yasa kika dawo kenan

Matsawa yayi yana ajiyar zuciya yace mutafi gida please babe

A bakin gado ta zauna tace wane gidan? babu inda zani banason in had'a ka da mahaifinka so.... please let me be please

Please Hanaan am sorry da sauri ta d'ago suka ha'da ido tayi saurin sunkuyar da kanta qasa ta fara kuka kusa da ita ya matsa ya zauna yanajin ajiyar zuciyarta hannunta ya dafa yace i..... love..... you Hanaan to the core i know i didn't deserve it i didn't deserve you but still janye hannunta tayi tace

"It's too late for that

Yace no it's not that late danyatsanta ta d'aga masa tace yanzun lokaci ya qure ka riga kayi aure da incigaba da zama dakai gara in rasa rayuwata

Har haka kika tsane ni?

Bakaga ka cancanci fiye da hakan ba ?magana zeyi ta dakatar dashi ta fice inda ta tarar dasu Anisa da Amal da ya Maryam a waje da gudu ta qarasa suka rungume juna da Amal zata fara kuka Amal ta rad'a mata kiyi haquri y'ar uwata suna kallo karki bari su mana dariya tayi saurin sakin murmushin yaƙe Amal tayi saurin goge mata y'ar qwallar data riga ra zubo

Ya Amina ce ta fito tace Hanaan mijinki zai tafi buris tayi kamar bata ji Maryam tace ance kinyi tafiya kardai yaji kikayi?

Cikin quluwa Hanaan tace haba ya Maryam saikace ke? maganar ta b'atawa Maryam amma saita hadiye tace ai gara ni inzama yayi da'di akan sab'a Hanaan tace to nikuma guri na basu shida amarya su shana

Kyaje garin basu guri su su baki

"Wa ya isa ya bawa uwargida guri?"

Hishaam ya fad'a tareda zama kusa da ita ya d'ora hannunsa akan kafadarta murmushi ta sakar masa yace love na saka kayanki a mota please muje gida na matsu wannan da kike gani itace uwargida kuma itace amarya ko don gaba

Babu musu ta tashi ta gyara mayafinta ya kama hannunta suka wuce suka bar Maryam tana baqincikin yadda suka dace da junansu

Tuqi yake amma gabad'aya hankalinsa yana kanta kamar zata gudu tunda suka taho daman gari yayi baqi saboda hadarin daya hado babu zato ruwa ya sauko da qarfinsa tunsuna tafiya harya tsaya sbd qarfin ruwan.

Shiru motar tayi inda ya kafa mata idanu kautarda kanta tayi ta kalli daya b'angaren sbd yadda ya mayence wa kallon ta hannunta ya damqe a nasa sam qin kallonsa tayi d'ayan hannunsa yasa ya juyo da fuskarta amma saita rufe idanunta sai hawaye ke sauka a hankali tsananin tausayin ta da sabon shauqin sonta ke shigarsa kallon ta yake cikeda tsanar kansa akan abubuwan da suka faru wanda duk laifinsa ne

Hanaan! ya fada tsigar jikinta ce ta tashi batasan meyasa ba duk lokacinda yakira sunanta takejin sunan daban a bakinsa qin amsawa tayi yace look at me please a hankali ta bude idanunta da sukayi jajir sabida kuka ta saukesu a kansa

A hankali ya matsa kusada ita yafara kissing d'inta abin ya ratsa har yatsun qafarta amma saita kasa hanashi wuyanta yafara shafawa da bayan kunnenta zuciyarsa na bugawa da qarfi

Tsanar kanta ce ta kamata ganin yadda ya maida ita batasan ciwon kanta ba
Hawayenta ne ya dakatar dashi ya matsa yana maida numfashi ya tallafo inda habarta ta lotsa irin nasa yace do you hate me that much?

Cikin sheshshekar kuka tace haqurin daka bani yayi ka'dan akan abinda kayimin

Babu namijinda duk rashin kishinsa zaiyi irin abinda kayi in kana son rabuwa dani basai kabi ta wannan hanyar ba ai yanzu dana aikata wani abu me zaka ce? shshhhhh yace tareda dora yatsansa a lebenta ban aikata hakaba ki yarda dani sam ban aikata ba nima tarko akamin na afka kamar ke nima victim ne

Na yarda cewar laifina ne sbd sakacin da nayi dake amma wlh duk abinda kike zargi a kaina banida masaniya ina roqin kibani lokaci da sannu zan fahintar dake kuma kisa wannan a ranki tunda aka kawoki gidana ban taɓa ko niyyar rabuwa dake ba

Bazan taba fahimta ba so please ka daina tabani sbd inason inyi aure clean batareda kowacce alaqaba tsakanin mu wanda ma akayi na rashin sani ya isa haka nan, a gabana kike cewa zakiyi aure? Kai kayi aurenma a gabana?

Ka takaleni ka cutardani akan na rama shine kayi amfani da ikonku na maza da Allah ya baku kayi abinda bazan tab'a yafe maka shiba.

Bakasan komaiba gameda quncin rayuwa, sbd kai ka tashi cikin soyayyar iyayenka ni kuwa sai kaka daga baya ma ta rasu na yadda da auren da ka yaudareni a kansa inda kaso da babu abinda bazan makaba amma saikaqi ma ka sani alayin matarka ka wulaqantani

Ai idan nacigaba da zama dakai banyiwa kaina adalciba sam tunda tafara magana girgiza kansa kawai yake tace mutafi ruwa ya tsaya.

Babu kalar gatan da banso nuna maka ba wanka kwalliya girki jan hankali ƙarshe ma dae na maka tayin kaina kacokan ba tareda kowace irin wahalar ka ba ka wulaƙanta ni kuma suk da haka na cigaba da kame kaina, haba nima fa mutum ce kamar kai kuma kamar kowa

Na sani

Amma fa kome zakayi sai ka sakeni Hisham.

Da mugun sauri ya kalleta jin ta gatsa sunan sa yau din hakan ya tabbatar masa da gaske take nufin abin da take fa'da din.

Please comment and vote 🙏🙏

Safiyyaa-z ✍️✍️✍️

Comment