KE DIN MATATA CE

Bismillahir-rahmanir-raheem

Kamar kullum yauma bayan sallar asubha karatun Qur'ani na nake rerawa a take na fara kuka mai sauti ganin rayuwa ta me cike da rashin ma'ana da amfani a gurin na kwanta har gari yayi haske

Qofar dakinsa dake cikin d'aki na na bacci na d'auko mukullin ta na bude a fusace ganina kawai yayi a dakin a kwance yake ko riga babu ajikinsa cikin magagi ya tashi zaune ya fara murza ido yana kallona cikin rashin sanin me nake sonyi

Koda ya wartsake ya fara qaremin kallo ban damuba saboda daman sana'arsa ce kallo na tashi zaune yayi sosai mur'dadden jikinsa ya qara bayyana his nipples are hard and pink

Da wasu layika a shafaffen cikinsa nayi sauri na kautadda idona, d'aga kansa ya sakeyi yayi ajiyar zuciya da qarfi yana kallo na da wata irin morning lust ya cije leben sa na qasa da qarfi cikin dashewar murya yace where are your manners girl?

Haushi ya kamani nafara magana. Nasan banida muhimmanci a gidannan amma inada muhimmanci a gurin wanda ya kawoni cikin rayuwar gidan nan

A zatona hakan shi zai zaunar dani a gidannan amma ina, na gaza da muzantacciyar rayuwar nan na sauka daga kan alqawarina na bazan rabu dakai ba.

Kukane ya fara qwace min,ina yi ina share hawaye na,na matuqar gajiya so ina ganin abinda yafi zan bar gidannan kafin nan kuma ka sakeni dukda ba'a matsayin mata nake agurin kaba niba jahila bace nasan da auren ka a kaina don haka ka sakeni nagaji da igiyoyin aurenka da ka daureni dasu

Kuma Kaje kayiwa budurwarka albishir da nabar rayuwarka har abada

Da sauri ya d'aga kansa ya dubeni nayi mamakin yadda naga maganar ta tsorata shi da yawa, nace eh bazan qara zama dakaiba don na gaji wulaqncin da kake min haka da sauri ya miqe ya damqi dantsen hannuna duka biyun ya fizgoni har jikinsa inda na razana a take musamman ganin yanayin sa ta tsakanin haqoran sa ya fara magana

"Tunda kika shigo rayuwata sanda kika so to sai sanda naga dama sannan zaki tafi ai na fad'a miki.

Nima kuma na gaya maka ni ba property d'inka bace banbancina da property kenan bakada iko dani,yadda naso nazo haka in naso zan tafi sbd bakada iko dani kuma bakada iko da jikina, cikani.........matsewa ya qarayi na rintse ido don azaba

"Kinason ha'da ni da mahaifina ne?bayan duk irin sacrifices danayi akan auren ki"

Eh a shirye nake da in ha'da ka da kowa don in rabu dakai kuma sacrifices da kake magana ai you did it for your own personal gain so don't blame it on me hannuwa na nakeson qwacewa amma ina qarfin babu had'i.

Na dubeshi nace you are hurting me hannuwan sa ya d'aga duka biyun kamar me surrender yace okay,okay na yarda zaki rabu dani nima zan rabu dake amma ban shiryaba kibani lokaci

Hanaan ta dubeshi cikeda takaici tace wata goma sha uku be ishekaba ko saboda kana zuwa gurin wata to ni babu wanda nake zuwa gurin sa.....

Yamutsa fuska yayi ya dubeta da fad'in

"ke ........me kike nufi?
What do you mean by that huh"?
To bari kiji in fada miki ko ke da kike mallakina bana saka ki a lissafina ballantana wata haramun karki kara zargina domin bakida hurumin yin hakan idan kuma kika qara zan tabbatar da na fanshe hakan a kanki yadda bazaki qara marmarin fadamin magana makamanciyar wannan ba kinsan inada qarfi da kuma ikon yin hakan, so advisable don't you dare test my patience again

Tsorata na fara yi kuma da abubuwan da yake fad'a d'in, na watsa masa wani mugun kallo,Ficewa nayi ban manta da buga masa qofa da qarfi ba

Tun ina shiryawa buhari yacemin yazo amma ko dana fito harabar gidan a tsaye na ganshi ta gabansa nazo zan gifta qofar motarsa ce ta tokareni

"get in"

"no thanks"

"don't test my patience"

"but you can't force me to get into your car"

Nayi maganar ina shouting

"of course I can"

"you can't"

"i can"

"You can't kuma idan natafi bazan dawoba"

Be saurareni ba waje yaje bansan me yace wa buhari ba, ko dana fito ya rigada ya tafi motarsa ya tsayar daidai inda nake ya budo qofar na zumbura baki na shiga ina qunquni

Har cikin makaranta ya kaini saidaya dangane da qofar ajinmu hakan yasa yan ajin suka fara ihu ana cewa saurayina ya kawoni kai kun dace kai kaza-kaza and so on

Can gefe na koma na fara duba mathematics ɗina sbd shi zamuyi first period yanayin shirun da naji ta ratsa class ɗin tasa nayi zargin math teacher ɗinmu yazo amma abin mamaki, koda na ɗaga kaina ya Hisham ke tsaye a bakin ƙofa da water bottle ɗina a hannu yana ɗaga zaren ta da yatsar sa yana min alamun in zo in karɓa ban san yadda akayi ba na kasa tashi daga insa nake kamar wacce aka riƙe wata fargaba da wata kunya ce ta kama ni ya maida ni saikace wata ƴar ƙaramar yarinya

Ganin banida niyyar tashi daga inda nake maimakon yayi tafiyar sa yadda nayi zato sai kawai ya sako kai cikin class ɗin inda ƙanshin sa ya fara cika ko'ina nan da nan gabana ya cigaba da faɗuwa inda babu abinda ƴan class ɗin keyi sai kallon sa musamman ma matan gaban seat ɗina yayi burki inda na kasa kallon sa sai ƴan kananan maganganu dake tashi can ƙasa-ƙasa ganin banida niyyar kallon sa ko magana yasashi ajiye ta a gabana Allah Allah nake ya fita amma kafin yayi niyyar fita math teacher yazo koda ya shigo saroro yayi da farko kafin daga bisani kuma abin mamaki ya saki rai kamar yasan ya Hisham ɗin

Hannayen sa ya tura cikin aljifan wandon sa ya juya kamae baison tafiya ya fara tafiya a hankali har waje inda math teacher ya bishi suka fara gaisawa suna magana cikin nutsuwar sa kamar koda yaushe duk maganar da suke baya dena kallo na tareda son haɗa idonsa da nawa inda hakan ya saukar da fargaba a tattare dani.

Babu daɗewa suka kammala tareda ƙara haɗa hannu alamun sallama inda ya maida shades ɗinsa ya shiga yaja motar sa ya fice ba tareda ya ƙara kallon inda muke ba

Tun bayan da aka fara lesson na fuskanci hankalin ƙawaye na gabaɗaya baya kan abinda akeyi ai kuwa yana gamawa tun kafi ya gama fita a class ɗin ihu da surutu ya cika ko'ina

yasmin tace amma naga kuna kama nan da nan idea tafado min nace yaya nane fa tace dan Allah ina sonshi dammm naji zuciya ta ta bada wani sauti kuma nasan dalilin yin hakan, narasa dalilin dayasa ya kawoni yau sam basu barni nayi karatu ba majalisa akayi qawayena kowa abinda yake fa'da daban kai dama akwai wanda ya dace da most beautiful girl d'in makarantar mu

Inda Yasmin tayi shiru can tace Hanaan ya kuke dashi kince wanki ne Hanaan ta fara inda inda tace he is my cousin

Do you love him???

There's no way in hell........

Yess!!! saida tasa kowa ya juyo saboda ihunta sai kuma tayi making sad face

Tace amma fa irin kallon dayake miki Hanaan kodai sonki yake shi??? Abin yayi yawa

Tsaki Hanaan tayi tace to yana da budurwa yasmin tace ai indai bake bace ba matsala

Saboda me? saboda in kece zan iya bar miki shi amma inba keba babu wadda zan iya barwa shi dariya abin ya bawa Hanaan ganin ƙarfin halin Yasmin ɗin amma saita gimtse tace aiko kyasha wulaqanci donko ya iya wulaqanci, babu komai bani numbarsa....

Zee ce qiri-qiri ta hanani bada numbarsa amma saidata bani wasiqa da alqawarin zan kai masa harda rantsuwa ta sakani abin ya bani dariya ganin yadda ta gigice a kansa daga ganin sa yau kaɗai ciki-ciki kuma gabana na ta fad'uwa

Ina dawowa daman lokacin dawowarsa be yiba kan gadonsa naje na dora masa wasiqar na fito na gudo ina tunanin me zaiyi inason inga yanayin sa lokacin da zaiga wasiƙar

Har na saka kayan bacci da daddare ina d'an shafa moisturizer sai kawai jin mutum nayi a dakina da sauri na miqe nayi crossing hannayena a qirjina sbd tsaro dariya ya fara harda rufe baki da bayan hannunsa yamin kyau sosai amma saina haɗa rai

Haushine ya kamani gani ya cigaba da dariyan kuma nace what are you laughing at? cigaba yayi nace "what's so funny" ? yace "chill there's nothing to see there I've told you" tareda nunani gabadaya na da niyya nayi in fita inbar masa dakin caraf ya riqeni ya jawoni kamar wata soson katifa har saida jikina ya ha'du da nasa babu komai jikin sa sai wani shorts sai black gym vest kusan duka jikin sa a waje yake da alama abin ya bashi haushi sosai inda hakan ya mini da'di sosai cikin hanzari na matsa baya wasiqar yasmin ya manna min ajikina yace meye wannan?

Murmushi nayi nace"wasiƙa ce, qarin masoyiya ka samu akan taka" a fusace yace kece me kawowa mijinki wasiqar wata? qarfina na ha'da don na tureshi amma sai ya kama hannun ya matse da ƙarfi don mugunta

Amma ban fasa faɗin abinda nayi niyya ba

"miji kuma"? Kuma budurwa ai saidai kayi qari amma daman ai kanada ita

"ke bakida kishine"?

Lebena na ciza na qasa harnaji zafi nace kishifa kace uh? Katab'a kishina? To why did I have to waste my precious time on someone like you?

Cikani yayi tareda dunguri na da yatsansa yace "What do you mean by someone like me huh?"

Kibud'e kunnuwanki da kyau ki saurareni by the time kika qara karbo wani saqo kika kawomin sai na gayawa kowa a makarantar alaqata dake....kinjini ko and you know i can do it right? "go-ahead...... am fine with that as long as zaka iya cewa ni property n kace"

Rainin dana barki kikamin ma is enough ba sai kin qara sa qawayen ki sun min wani ba

Zangaya musu ke mata na ce. mamaki abin ya bani kafin nayi magana ya bar dakin au daman yasan ni matar sace?

Yanzun bana bari mu ha'du balle yace zekaini makaranta

Yau yayansu yasmin ne ya kawomu gida sauri nake sbd ina zargin lokacin period dina yayi da sauri na shige gida daqyar nayi bacci sabida marata yanzun abin qaruwa yakeyi kullum

Yana zaune a office yau sbd yayi aiki ya gaji gashi har lokacin yana tsaye zamansa kenan bayan theater 7 hours da sukayi ko kayan theater be kaiga cirewa ba wayarsa ta dauki qara leqawa yayi don ganin sunan dake yawo kan screen din, ai da hanzari ya daga ganin me kiran nasa

Abban sa ne Bayan ya gaisheshi ya sanar dashi ya koma gidansa yanzu za'a kawo Hanaan gida sbd batada lafiya an kira daga makarantar su

Besan meyasa ba maganar ta dake shi sosai cikin hanzari yake tuqin yana ganin kamar baya sauri tareda fadin me yasameta hakan.

yana zuwa motar makarantar tana tafiya da sauri ya shiga part d'inta ya wuce kai tsaye a qofar bedroom dinta yayi karo da takalmanta da d'an hijabinta a rigingine ta kwanta kanta yana lilo inda gashinta ya zubo har qasa

Da sauri ya qarasa inda take a gefen kanta ya zauna ya fara dubata cikin hanzari kamar yana son ya rikice

"meke damunki?

Ido kawai ta bishi dashi duvet din ya janye da qarfi fararen cinyoyinta suka bayyana kasancewar ta cire skirt d'in uniform d'in yayi saurin rufe idonsa sbd yanayin dayaso shiga cikin qanqanin lokaci kullum baqin al'amura yake ji kuma yake gani a tareda ita amma abinda yafi komai bashi mamaki ai idan zai duba patients d'insa baya jin hakan to meyasa yanzun?. Rana ta farko daya tab'a rayawa ransa cewa ita d'in mace ce

A hankali ya bude idonsa cikin son ya sake ganin abinda ya haifar masa da bugun zuciya da sauri amma kash taja duvet din cikin rashin qwarin jiki ta rufe zuwa kwankwason ta kallon ta yake ta lumshe dara daran idanunta red lips d'inta yake kallo suna tempting nasa how he wish to kiss the hell out....

"Stop.... stop staring",

Shaquwa yafarayi "fucckk" ya fa'da a hankali ganin ta kamashi

Inane ke miki ciwon? tareda shafa kanta a hankali continuesly cikin son yayi hakan,ture hannun sa tayi

Is that how you treat all your patients?

Be kula ta ba be kuma d'auke hannun sa ba sai ma ya amsa tambayar ta da tasa tambayar

"Ina ke miki ciwo"?

"Ba ko'ina"

Qara yaye rufar yayi, ai da sauri ya miqe ganin yadda tasa mayafinta ta tamke cikinta kwancewa ya fara yi da sauri yace "zaki cutar da kankifa" da qarfi yayi maganar sbd ya tsorata da abinda tayi d'in

Kina ciwon marane? fuskarta ta rufe da bayan dantsen hannun ta (back of her wrist) sannan ta d'aga kanta a hankali alamun eh wasu zufa suna tsatstsafa a goshin ta kallon ta yake cikin mamakin abinda take yi meye abin kunya a monthly cycle "daman yana miki hakane? kai kawai ta sake d'aga masa tare da alamun zatayi kuka

yace

"you are so childish"

Dagata yayi cak ya zaunar da ita ya koma d'akin sa ya debo wasu magunguna ya dawo ya bata maganin tasha ba'a jimaba tafara kwarara amai duk yabi ya rikice wrist watch d'insa da be da'de da mayar dashi ba ya sake cirewa ya matsa ya kama ta ya kaita toilet yana qoqarin taimaka mata

Amma Sam taqi ta rufo qofar tunda ta fito da bathrobe yake qare mata kallo ganin yadda fatarta take qyalli ga gashinta ya manne a wuyanta da fuskarta tana tafiyar sannu a hankalin kaman bazata iya taka qasa ba

Gyara gurin yayi yace ya kamata a samo helper ,tace no thanks indan yau ka kwashe amai ne nayi irin sa yakai sau goma sha uku a gidan ka wannan kawai ka sani tunda Ayya ta rasu nake kula da kaina ni da zaka rage mazan daka cika gidannan da sunan ma'aikata ma da yafi sauqi gida duk maza ni ka'dai mace?

Kaya tayi niyyar sawa amma yaqi tafiya kwanciyar ta tayi ta rufa sbd ta farajin yanayin zazzab'i sosai

Tunani ta barshi yanayi abinda kuma yafi damunsa yanzu duk wata haka take shan wannan wuyar amma ko labari bashida shi ga yarinyar da dauriya abinda be iyaba a rayuwar sa bayajin zai iya barinta ita ka'dai don komai zai iya faruwa da ita

*******************
Da daddare
Kuka take sbd azaba ga kewar Ayya ko tashi ta kasa yi ballantana ta taimaki kanta sai marar kawai take dafewa qofar dakin ya bude a hankali ya shigo

"kinyi bacci ne"?

Shiru tayi masa kamar tayi bacci tana cije baki sbd azaba kusa da ita ya zauna hucin jikinta yaji yayi saurin yaye rufar, dagata zaune yayi ya jinginata da jikinsa yabata magani tasha

Zamewa ta ƙara yi ta kwanta a gefen jikin sa tareda kamo hannunsa ta ɗora saman marar ta ta danna da ƙarfi tace "danna min Please banida ƙarfin dazanyi da kaina" saurin janye hannunsa yayi yace "this is not the right thing to do"

Ruwan ɗumi ya samo ya ɗauko clean towel a wash room ya tsoma a ciki ya matse kaɗan ya kwance rigar tata ganin pant ɗinta da ƙasan ƙirjinta na neman fitowa yasa shi kawar da kansa gefe sbd tsaro.

Inda ya laluba ya fara danna mata ruwan ɗumin sannu kan hankali daɗin hakan na ratsata inda da ta fuskanci ya matse saita kamo hannunsa ta dannan a gurin har bacci ya fara ɗaukanta sbd ta galabaita

Gashinta daya mammanne mata yake gyara mata yana kallon ɗan ƙaramin bakinta data turo gyara kwanciyar ta tayi sai kawai yaji cikinta yana ƙugi da alama yunwa ce. Kallo ya bita dashi komai nata na mata amma fa yara ko a toilet ya fuskanci panties dinta pink colours daga Hana Montana sai Barbie da sauransu haka pad din ta ma sai wani irin qamshi da sukeyi mai saukar da gajiya

Kitchen yaje cikin sa'a ya sami ragowar soup ya dumama ya kawo mata daqyar ya tashe ta tasha ta kwanta daya gefen ya zagaya zai kwanta ashe batayi bacci ba ta juya cikeda rashin kuzari murya qasa-qasa tace

"Doctor, what are you trying to do"?

"Can't you see, I'm trying to have some sleep".

Whaaaat?,here?

Cikin rashin kuzari ta yunqura ta zauna tace gaskiya bazan iya kwana dakaiba murmushi me sauti yayi yace meye anan balle a dauka? baki yadda da kanki bane

na yadda da kaina kaine dai ban yadda dakaiba

Nan d'akina ne

nikuma nan gidana ne

marairaicewa tayi please banida qarfin fa'da dakai a haka nake rayuwata a gidanka.

Ahaka kuma kikeson kicigaba da rayuwarki?

Shiru tayi sbd batason ci gaba a hakan yau ganinsa ka'dai yasa ta sami sauqi fiye da da sosai juyawa tayi ta kwanta tana qunquni

"i don't want anybody's sympathy"

Har ya fara nisa a baccin sa yaji ta fara kiran sunan Ayya a hankali tausayinta ne ya kamashi gashi jikin ta na rawa ya matsa ahankali ya jawota jikinsa bacci take besami matsala da hakan ba zafin jikinta ke shigarsa da wani sabon yanayi daya sauka, rikicewa ya nemi yayi sbd be ta'ba kusanci da wata ba kamar yadda yake a yanzun qoqarin tashi take hakan yasa ya rufe idanunsa karta masa tsiwa

Ahankali ta fara bude idanunta jin mutum kusa da ita a kansa idanuwanta suka sauka dim light din dakin ta bata daman qare masa kallo dama dae Ace wannan ba tausayi bane so ne, da nafi kowacce irin mace sa'a a duniya abinda take saƙawa kenan

Gashin idonsa dake matuqar burgeta ta shafa ahankali ta sauko kan hancinsa tana shafawa ahankali ta sauko ta shafa bakinsa ahankali ta bude idonta dayake qoqarin rufewa da kansa ga zazzabi tana ji ta kafawa lebensa idanu ko ba'a fadaba tasan takamu da sonsa tuni amma bata tsammanin wani abin kirki daga gareshi koda yasan hakan bata tsaya tunani na biyu ba ta matsa ta ha'da hancinta da nasa tana shaqar qamshinsa datake masifar so tana goga hancin su a hankali

Kamar numfashinsa zai dauke yarinya qarama tana neman ja masa aiki a lokacin da take goga hancinta da nasa numfashinsa ya nemi ya sarqe labbanta da yaji akan nasa shi ya dolanta masa bude oily eyes dinsa a gajiye kallonsa take idonta a nasa inda yake faman ƙifta idanun sa nonstop sbd abin yayi shocking ɗinsa gabaɗaya, ita kam cikin nutsuwa take kissing dinsa inda ya zama kamar wani soko kallo kawai yake binta dashi amma abin yana ratsa duk wata kafa ta jikin sa musamman yadda take shafa gashin dake kwance a fuskar sa da dukkan hannayen ta da yadda ta nuna son abinda takeyi ɗin hakan ya saka shi runtse idanunsa da karfi tayi tsammanin hakan daga gareshi sbd tasan bazai ta'ba bin ta tata ba daman, kamar sweet haka take jin lips ɗinsa a hankali take sucking har saida taji ta fara gumi alamun zazzabin ya tafi ƙasa tayi da lumsassun idanun ta  ta fara janyewa a hankali daga jikinsa a hankali tayi murmushin ganin irin shock ɗin data sashi a ciki lokaci guda har yanzun idon sa na kanta kunya ce ta lullube ta ta juya bayanta a hankali tana sauke numfashin ta inda shima yake ajiyar zuciya akai-akai kuma a fili

Ya dade yana kallon bayanta he needs more abinda zuciyarsa ke fa'da kenan be taba experiencing abu me makamancin da'di irin wannan kiss din ba her lips were so soft, so warm and so sweet yana kwatanta ranar da zai fara kissing Shukra amma be taba tunanin zaiji hakan ba sam sam amma sai ya gimtse ya shafa kansa

"She stole my first kiss, and instead of being mad at her I found myself enjoying her lips

"Hmmnn after all young lady, you are not afraid of Hishaam you are afraid of yourself, you don't believe in yourself at the first place kenan ko"

Gara in tafi daga nan karki canza min ra'ayi

Abinda yake faɗi a zuciyar shi kenan inda a zahiri kuma

miqewa yayi zai fita

"thanks" tace ba tareda ta juyo ba

Wani nervous murmushi ne ya subuce daga lips d'insa da besan ya yi ba

yace "night"

tace "good night doc"

Good night sweet one ya fad'a a zuciyar sa

Gabanta ne ya cigaba da faduwa ta dafe tana fadin mena aikata haka daman yana ganin banida kunya shikenan rintse idanunta tayi harta samu bacci yayi awon gaba da ita

Kwana yayi yana mamakin yarinyar kar ko dai ....aa haba dai karma ta fara

Kodayaje dubata da safe abin ya bashi mamaki har break fast ta ha'da tayi komai kamar ba itaba kallon sa take ya matuqar yi mata kyau green shirt ce ajikinsa da black wando jeans da black jacket sai wani green shawl....

"Are you done checking me..... out....?

Fuskewa tayi sbd ta fuskanci da'di yakeji a duk lokacin daya kama ta tana kallon sa tace ina kwana mamaki ya bayyana a fuskar sa yace daman kin iya gaida mutane? ta basar tace bismillah ga abinci kamar yaqi ci ya tuna kullum saiyaje gida yau idan yaci anan ya huta

Komai yayi dadi chips din ya soyu yadda yakeso saidai soup en yayi yaji ruwa kawai yake kwankwad'a dariya take sonyi masa yace thats not funny fa, tace saikace yaro jiba yanda yaji ka'dan yasaka gigita inda babu shiri dariyar ta subuce gaba daya

Tunda ya fito lips din ta yake jarabar kallo yana mamakin abinda yaji daga garesu

Sauri yayi Ya miqe yana fadin kisha magani akan kari zan neman miki appointment gurin dr hadiza tunda field enta ne saiki ganta____kuma...... in kika ƙara bani anything too spicy a bakin nan naki zan goge shi tass ya shafa leɓanta da yatsansa inda hakan yayi mata bazata ta warware idanu tana bin hannun nasa da kallo kafin tayi magana ya fice da sauri sosai

Yatsan sa yayi kissing wanda ya gogo lips d'inta dashi ya rasa dalilin hakan da yayi

Yau koda yaje gida beci abinci ba bayan ya samesu a dining sai a lokacin suke qoqarin fara breakfast Mom ya fara gaisarwa ta amsa masa cikin qauna da kulawa tanajin dad'in yanayin sa na kwana biyun nan ni'ima ya kalla yace bazakice ya jikin qawarkiba? gabadayansu ita da Mom suka juya suna kallonsa kafadarsa ya d'aga alamun tambaya irin me ya faru kuke kallona dinnan

Ni'ima tace lallai yaya kana jida Hanaan kodan yau ta baka abinci? Ni ba qawata bace

Idan ba qawar ki bace ai ke kika rasa don ita zata haska ki ba ke zaki haska ta ba mara kunya kawai

Au dagaske kaci abincin ta lallai Kam yau anci jagwalgwalo

"kece zakice mata jagwalgwalo to wlh ta iya girki yadda bazaki ta'ba iya kamotaba garama kisan me kike ciki "

Mom kallon sabon yanayinsa kawai take haushi kamar ya kashe ni'ima saboda ta fuskanci yaya ya fara tarewa matarsa tace to wlh samarine da ita a ajinmu... da sauri ya galla mata harara ta gimtse abinda ta fara fa'da inda babu zato hakan ya faɗar masa da gaba

A wajen aiki office din shukra yaje yanason suyi magana kasancewar tanada ragowar patient yasa shi jira bayan sun tafi ya fara mata magana shukra ina ganin abar maganar auren nan for now....

"Saboda me?"

Saboda bazan iya adalci atsakanin mata biyu ba tunda na kasa yiwa dayama

Ki duba kiga yarinyar nan batada lafiya amma ko sani banyiba for almost more than a year shukra ina tsoron karya dokokin ubangijina kuma ina tsoron shiga wuta

Daman kuma yaudarar ta nayi na aureta ranar dana bata labarinki saida tayi nadamar aurena a take, banason incigaba da aikata sabo da gangan

Ka yarda ka kamu da sonta yanzun? bansaniba ko inasonta abinda nasani shine akwai wani abu tsakanina da ita da bazance gashi ba kuma bazan iya sakin ta ba sbd zai zama rashin adalci a tare da ita kuka shukra ta fara

Shukra ki d'auka qaddararmu Kenan don yanzu innace zan rabu da ita zaizama kamar rashin adalci kuma hakan ba yana nufin mun daina zumunci ba kenan.,...

Hishaam kabar zancen nan kawai kabarni ni kadai for now please ba musu ya fita yaja mata qofar

Dariyar idris ce ta katse Mata kukan daga bayan labulenta ya fito yana tafa hannu yana dariya yace me na gaya miki? kika karyata ni shukra ta goge hawayenta tace aidaman nasan halinsa indai akwai wani abu saiya fa'da donshi besan wani abu b'oye b'oye ba

Amma kaicon Hishaam sam banso shigarda boka cikin al'amuranaba saidai kashh yayi gaggawar sanar dani nasa tsarin nikuma yanzu ko bayaso saiya aureni

Dariya Idris ya qarayi yace gaskiya babu adalci ki nace kice kamammen mutum kamar Hishaam da ko hannun mace be tab'a kamawa ba kice saiya auri ragowa irinki a hasale shukra tace kai shashasha yamuke dakai dakake harin qaramar yarinya bayan kasan halinda rayuwarka ke ciki Idris yace garani aure tayi ta rabuda mijin zan aura kekuwa ragowace ba auren kikayiba amma gara bazawara dake

To yanzu a ganinka zai saketa bayan munyi sakaci dagani harkai to duk waye ya jawo?nice amma yanzu zangyara komai inmun gama komai da hadiza za kaji zancen.

*******************

Ciwon marar ne ya dawo yauma ruwan dumi tasha ka'dan ta kwanta tana jira ko zai shigo.

Bayan yasa kayan baccinsa wasu masu taushin gaske gasu farare tas a hankali ya tura qofar dakin irin kwanciyar jiya tayi amma yau ta d'aure gashinta kusada kanta yaje ya zauna ahankali ya lura ta rame ka'dan yace kinji sauqi? ta girgiza kai murmushi yayi yace ke wace irice?

Qarya kakeson inyi? Amma at least saikice alhamdulillah to alhamdulillah. Yawwa ko kefa ribbon din kanta ya zare gashin yayi qasa saurin tashi tayi da fad'in lafiya?

Yafi kyau a hakan blushin ta fara tana dafa kumatunta

"Sai kikayi kama da bararoji"

Turo bakin ta tayi tana hararar sa,matsawa tayi kan pillow ta kwanta tace asubha ta gari kusada ita ya matsa ta zazzaro masa ido yace wa zaki gayawa ido shima yafara zazzaro mata nasa dariya ce ta kamata ganin ya maida kansa yaro kamar ita

Matsawa ta sake yi amma yana sake matsowa hartakai qarshen gadon hannunta ta miqe ta tokare qirjinsa tace ya isa hakanan qasa-qasa yayi da murya kamar zai mata rad'a yace

"Hey if you don't mind i can help you"

Cikin sonjin wane taimako zaimata tace wane treatment ne? inaso me zaka bani? gyran murya yayi yace

"If you want we can have... a.... s-word cikin rashin fahimta tace what does this s-word means?

Dariya yayi sosai harda dafe ciki saidaya gama yace how old are you?

"Seventeen"

Da confidence enta wata dariyar yafara yanason rufe bakinshi haushi ya kama Hanaan tace bansan kanada yawan dariya ba sai yanzun

Yace seriously... shekarunki sha bakwai kad'ai? tace yep! yace shiyasa bazaki ganeba kunnen ta yamatso yarad'a mata s-word means sex, we can have a sex a slow ta juyo ta fara masa wani kallo me cike da ayiyin tambaya

"For your sake"

Tureshi tayi tace Allah ya kiyaye tareda rufe fuskarta da duka hannayenta. mamakinta yake sosai ganin yadda taji kunya da tsoro akan d'an abinda ya fada be qarasa tunanin saba tace amman yau a dakinka zaka kwana ko? Saboda me?

"I need some privacy"

"Mhm su privacy manya, yafada yana kwaikwayonta haushi abinya bata tashi tayi ta dauki pillow zata koma kan kujera ta kwanta

Yace take it easy girl ki take the bed I'll take the couch, ba musu taja bed sheet din data nannade jikinta dashi ta koma yana hardeta kallon ta yake yana dariyanta

Gabad'aya abinda yake zargi akan tarbiyyar ta ba haka bane irin kallon da yake mata sam ba haka take ba kenan Abbansa yasan hakan shiyasa yayi masa sha'awar ta tun tuni sam bata qoqarin yi masa shishshigi a al'amuran sa daman ya tsani hakan shiyasa bayayin y'anmata sam sbd mace tana kulashi ko ta cika nace masa to ya sakata a sashen marasa aji ita kuwa akwai tsira da mutunci

Ko da Ya fuskanci tayi bacci lallabawa yayi kan gadon ya kwanta yana kallon fuskarta mecike dakyau da kwarjini yana tunanin daren jiya tsigar jikinsa ce ta fara tashi ya fara jin jikinsa yana reacting

"damn my hormones" ya fad'a a hankali

Juyawa yayi amma ya kasa bacci saida kyar bayan ya rungume ta ta baya da alama bacci take sosai lif yayi a jikin ta nan da nan bacci yayi awon gaba dashi.

Ba sallah zata yi ba shi yasa bata tashiba har gari ya fara haske ka'dan huci takeji kusada ita muskutawa takeson yi amma kamar an daureta daqyar ta bude idonta mamaki ne ya cikata ganin yadda suke kwance qafarsa ta hagun akan qafafunta kansa akan kafadarta ita kuma tana kan hannunsa na dama na hagun kuma shit..yana kan cikinta ko kuma fatar cikinta a cikin rigar ta qugi cikinta ya farayi zuciyar ta ta fara abinda ta saba

Qura masa idanu tayi bata ko qyaftawa motsi ya fara tayi qoqarin ta matsa amma ina, ko motsin kirki ta kasa yi a hankali yake bude idonsa rufe nata idon tayi kamar me bacci qura mata ido yayi yana kallon tsabar kyawunta gabansa na faɗuwa sosai, tabbas tafi dayawan matan daya sani komai da ake kira kyau she's the real definition of beauty halayen da yake kwadayi yake zargin bata dasu suma a hankali ya fara samun su

"Perfect" yace a cikin ransa

Yanayin su ya kalla sai yayi murmushi tunawa da batasan ya kwanta a jikinta ba, hannun sa ya kalla a cikin rigarta a hankali ya sake shafa cikin ta tsigar jikinsa na tashi.

Runtse idanunta tayi sbd yadda yanayin ya shige ta hancinsa ya goga a wuyan ta yanajin daɗin ƙamshinta na wani abu da take amfani dashi me strawberry kamar aci ya ɗaga kansa yana kallon lips ɗinta da yake so ya haɗiye yawu qutt.

Kamar ya tashi amma ya kasa matsawa ya ƙarayi ya manna mata Kiss, a goshinta murmushi tayi ta gyara kwanciyar ta da alama tanajin daɗin baccin ta. Inji shi fa 😜

Kyau tayi masa ya ƙara matsawa yana ƙare mata kallo yana jin zuciyarsa na wani irin bugu inda itama Hanan kejin hakan, kamar wanda magnet ke ja ya ƙara matsawa har saida ya haɗa le6ensu guri guda.

A take gashin jikin sa ya mimmiƙe ya kasa janyewa ya kuma kasa komai yana kallon ta jikinsa yayi wani irin sanyi gaba ɗaya.

Kasa komi Hanan tayi itama zuciyar ta na azalzalar ta tanajin kamar ta janyoshi jikinta sosai karya fasa abinda yayi niyya koba komai zata rage jin kunyar Kiss ɗin data masa itama.

Abinda yake mata shi ya katse mata tunani tareda kasa daurewa ta buɗe idanunta instantly, leɓenta na ƙasa yake tsotsa a hankali cikin nutsuwa tareda matse ta gam a jikinsa kamar yana tsoron kar a ƙwace masa ita.

Idonta ta waro hakan yasa ta ɗan buɗe bakin ta kaɗan cikin ɗumbin mamaki hakan yabashi damar shigar da bakinsa gaba ɗaya cikin nata yana smooching lips ɗinta ƙasa da sama tareda zura harshensa cikin bakinta yana yi yana shafa cikinta da hannun sa dake cikin rigarta har yanzu , inda tayi saurin runtse idanunta tareda damƙe rigarsa data kama sbd wani irin yanayi da take ji .

Tsoro ne ya dira a ranta lokaci guda musamman ma data tuna ita ɗin ba kowa bace a gurinsa bata wuce abar wasan sa ba.

Da kansa yaga abinda yake yi ya fara wuce ƙaida yayi tumanin kar yayi tafiyar da tsaiwa zata masa wahala janyewa yayi a hankali tareda saurin matsawa yana kallon ta numfashinsa na fita da sauri da sauri,yana jin yadda yake shiga tsananin son kasancewa tareda ita, tsananin son ya jishi a jikin ta, saurin tashi yayi yana janye hannunsa ahankali tareda kallon idanunta data runtse su taƙi buɗewa yana shafa sumar kansa gami da lashe lips ɗinsa da yake jin test ɗin nata akansu .

Tunda ya fita yake mamakin abinda yayi, ji yake kamar ba shi bane yau banda tunanin ta kuma babu aikin da yake faman yi har abin ya fara bashi haushi "she's just seventeen, mtsew what's wrong with me"?

Nothing yabawa kansa amsa, koda yake ai laifin ta ne ba nawa ba sbd ita ta fara hakan ni kawai ramawa nayi. Murmushi tunanin ya bashi yana tuƙi yana murmushi har ya isa

Koda yaje asibiti wajen hadiza ya wuce ya farayi mata bayani. "Hishaam kasani basai na maka bayani ba kuma auren nan fa ya dade ai ya kamata ace kayi wani abu kodon lalurar nan ga Maryam har yarinyar ta ta fara wayau"

Hisham yace You know..... at this stage she can easily get pregnant and she's too young for that. Amma it's for the better ai zatafi samun sauqi fiyeda yanzu

Amma idan babu damuwa zanbaka maganin hausa sai ka kai mata,

"Nifa kinsan bana shiri da abinda bayada k'a'ida"

"Eh amma ai ita tanada, tunda Ayya ke karba mata in kayi mata bayani tasan maganin ai idan tayi wanka zata fara sha

Kawai dondai kince ta sanshine amma da gaskiya bazankai ba.

Nifa dad'i na da kai rashin kunya, nifa surukar ka ce

Banza yayi mata

Hishaam ga shayi

A'aa yau kuma harda shayi inada aiki badan hakaba da nasha

To ka tafida flask en mana saika aiko dashi na sanka akwai son shayi gadon buzaye

Ba musu ya d'auka tareda yimata godiya ya fice

Da sauri shukra ta fito daga inda ta buya suka rungume juna tana fad'in munjefi tsuntsu biyu da dutse daya to sauran aikin idris kuma Allah yasa zai iya.

Har wasu awanni suka shude tunanin ta kawai yakeyi hakan ya tilasta masa jan sumar sa da qarfi
"This girl is messing with my head"

Wani tunani ne yazo masa yanzun haka y'an makaranta suke kallon jikin ta da yafi komai daraja a gurin sa idan kuma wani shima yana son lips d'inta kamar yadda shima yake son su fa ya zaiyi?

Wani yaji yaji a ransa daga wannan tunanin

Ko dai haqura da karatun nan za'a yi kawai??

Kai ban isaba nasan Abba bazai bari ba

Gashi basu san ma matar aure bace kenan zata iya yiwuwa ma tana da samari

"Damn it, fuck the school and f*ck the boys bushashshen leben sa ya lasa yace

"Things are getting hard to handle"

Be gama abinda yakeyi ba ya tattara ya fice, directly makarantar su ya wuce sanin yau din ta dage zata je makaranta bayan yace kar taje, lokacin da ya je qofar ajin su basu tashi ba hakan ya tilasta masa zama a mota

Befi ten minutes da zuwa ba suka fara fitowa qofar fitowa yake kallo da son ganin ta inda zata fito duk wacce ta fito sai ta qare masa kallo inda hakan ke sashi qara tsuke fuska

Can yana zaton ma sun gama fita sai gata nan abin mamaki babu ko takalmi a qafar ta babu socks suna riqe da hannu ita da zee. Kyawawan qafafun ta yake kallo abin haushi har zuwa qaurinta a bude yake kowa yana gani

"Wai ita batasan jikin ta ba irin na kowa bane batasan jikin ta ba nata bane ba? her body is not longer her's a lone"

✍✍✍

Sunkuya wa tayi tareda dafe marar ta da cijewa alamun har yanzun tana jin ciwon da sauri na fita amma kafin in qarasa ta miqe kamar in qarasa sai kuma na tuna duk taron yara ne a gurin.

Ba qaramin tashi hankali na yayi ba lokacin da naga ta tafi zata fa'di, amma lokacin da naga babban tashin hankali shine lokacin da wani yaro wanda ba zaifi sa'an ta ba ya rungumo ta ta baya gabadaya sakamakon riqo ta da yayi ta baya a lokacin da tayi baya zata fadi.
Ban taba sanin inada zafin nama ba sai yanzu a gurin na tsinci kaina na janyo ta jiki na zafi jikin ta da alamu harda zazzabi tayi saurin bude idanunta inda ta cika da tsoro da mamaki hannu ya miqo zai qara ta'ba ta ban tsaya komai ba na sharara masa mari ya dafe kumatun da sauri da alama marin ya shige shi nan da nan aka fara surutai a gurin.

Ban jira komai ba na jata zuwa cikin mota na jefa ta na rufe ban kula da halin da take ciki ba na shiga na tada mota muka dau hanya ac ce a motar amma zafi na dinga ji sbd masifar danake ji a raina kuka take inda hakan ya qara tunzura ni

Why did you let him touch your body.......why???

Tun daga bakin layi nake horn inda me gadi yayi saurin bude qofar na shiga a guje a qofar part din ta na tsaya kafin in fito ta fice da gudu kamar ba ita take faduwa a hannun wani ba yanzun, da sauri na bita inason inji me zata ce kuma

Tana kwance rub da ciki na shiga d'aga ta nai akan gadon akan gwiwoyin ta

"Wannan ne karo na farko da haka ta faru ko kuma daman suna ta'ba jikin ki"?

"Me kake nufi da hakan"?

Ina nufin haka kowa yake ta'ba jikin ki baki san jikin ki yana da darja bane"?

"Sbd me yake da daraja kuma idan ma yana da daraja ai kwalliya ta biya kudin sabulu tunda an hanashi ya ta'ba qasa ko kana kishi ne"!

"Akan me zanyi kishin ki ke da bakya kishin kanki kina barin kanki sakaka a wajen kowa"

Ba dai kowa ba shi wannan na daban ne sbd shi yana sona kuma nima............

HANAN ✍️
*******
Babu zato naji ya janyo ni daga kan gadon ya matseni tsakanin hannayen sa and then he kissed me hard naji wani irin zafi ya ziyarci labbana ina qoqarin tureshi yana ci gaba da abinda yakeyi azaba ta isheni na kasa qwacewa qwallar da nake matse wa ce ta gangaro yayi saurin cikani fuskar sa na tafi zan mara da iya qarfi na ya riqe hannun cikin zafin nama.

Hakan ya hasala shi rufe idanu na nayi ina jiran ta inda zai fara lallasa ni amma sai kawai ya qara kamoni kamar wata abar wasan sa ya dora lips d'insa tun qarfi akan nawa ya cigaba daga inda ya tsaya ture shi nayi da iya qarfi na na sake d'aga hannu don marin fuskar sa ba tare da tunanin ko zai kashe ni ba ko zai barni da raina.

Hannaye na ya kamo ya matse a qirjin sa ya janyo jikina gaba daya ya matseni da hannun sa daya dayan kuma yana riqe da hannaye na yana qara kissing dina sai kace wata karuwa mara daraja hakan ya bani dama na juya fuska ta gefe cikin qyamar abinda yakemin don kansa ya cikani na qara daga hannu ko zanyi sa'ar marin fuskar sa this time around sai kawai ya turomin fuskar sa gabadaya

"Mareni mara kunya"

Fuskantar hakan nayi kamar dadi yake masa sbd ni torture ce a gareni shi kuma bazan ta'ba samun dama a kansa ba sai na canza shawara sbd nasan me zaifi bata masa rai

"Duk abinda ka gani haka yake, da duk abinda kake zargi ma haka yake sai meye? kai dana amince da kai ma a matsayin miji kake zuwa wajen wata ballantana ni da nake ungulu ba kazar kowa ba, kuma ka sani bakada ikon da zakayi kishi akaina ko akan duk wani abinda ya shafeni ko kuma jikina"

Kuma ka sani wannan yaron daka mara yana daya daga ciki.,......

Hannaye na ya kama inda na fara qoqarin tureshi ya riga ya riqe gam

"Ki dena cewa zaki gwada qarfin ki da nawa sbd kinada tsayin qafa kawai

Hakan ya zama kamar kokawa inda nayi baya yasa na fada kan gadon shi kuma yana sama na

Kallo ya fara bin fuska ta dashi da tayi jajir sbd kuka yana shafa lebena ya taho zaiyi abinda yafi so nayi saurin kautadda kaina gefe y'ar dariya yayi data fito daga qirjinsa ka'dan

"Your lips are swollen as hell"

Doke hannun sa nayi cikin tsanar sa
"Ba ungulu ba ko mecece ke din mata ta ce ke din akwai me ke kinji ko"

Ci gaba yayi da shafawa a hankali a hankali sai kace wani zautacce kuka na fara na kautadda fuska ta daga saitin sa nace "please ka sake ni, na gaji da zaman gidan ka bani da wata daraja a wajen ka har ma gara da akan yanzu"

Yi yayi kamar bejin maganar danake fad'a pecking lips dina yayi kadan da fadin

"Wannan marin da kike qoqari sai kinmin yayi ka'dan ya zama sila sai kin sake dabara tukunna sai ranar da kika yi qoqari kika mareni da gaske tukunna sai lokacin ne za'a ayi maganar a lokacin idan dabarar ki tayi zafin naman ki ya kai sannan kinji ko? yanzu bakida zafin nama ko kadan?

Gashi na ya fara shafawa inda yasa yatsar sa yana wasa da karan hancina ya kama hancin yana ja a hankali yana magana tareda quramin idanu

"Karki qara maganar wani a gabana kinji ko inada kishi inajin haushi sbd ina kishin ki sosai komai naki nawa ne ni kadai ni kadai kinji? uhmn?"

Kinga na taimaka miki sbd kin motsa jiki zazzaɓin ya sauka tareda taɓa goshina yana taɓa nashi lokaci guda

Baki yabar ni dashi a bude sbd mamakin sa na fara galla masa harara jin abinda yake fada din

"A ina ya zama nakan ba kowa bace ni a gurin ka ai da bakinka ka fada ba wanda ya matsa ka" ture hannun sa nayi daga goshi na da faɗin au daman kasan ina zazzaɓi??
Be bani amsa ba ya cigaba da magana

"Kuma yanzun dole a sami dogon wando na zuwa school ko kuma a dena school din"

Banza nayi masa tareda qara galla masa wata hararar

Tashi yayi yana gyara rigar sa data dade da fita daga hayyacin ta, sbd saida na tabbatar tayi squeezing na kuma cire duk wani button da yake jikin ta,ƙirjinsa yake kallo vest ta rage masa sbd shirt ɗin ta gama yawo yana kallon jikin sa yana kallona da wani mischievous smile ya fara tafiya har ya fice daga dakin

Zugum nayi na rasa me yakemin da'di da babu ruwansa dani shiyasa zaman yayimin sauqi amma yanzun abun ya fara gaba ni kuwa bazan zauna dashi kullum ina fargabar kar ya cuceni ba tunda nasan ba sona yake ba.

Hannaye na nasa a fuska ta na fara garzar sabon kuka na cikin yanayi na damuwa da kuma rashin lafiya.0

Ya Allah.

Please comment 🙏

Safiyyaa_z

Comment