MR & MRS HISHAM BAITA

HISHAAM
**********
Sam haushin yarinyar nakeji tun farko ganin na bata satar amsa amma ta kasa tace bata son auren abu na biyu sam yarinyar batada kunya shekaruna sun kusa ninka nata amma a gaban shukra take wani dokemin hannu da wasu awful figures din ta Allah na tuba bana saka irin su a mata ababen sha'awa bayan ma maybe an saba ta'ba ta amma harda dan show up din ta.

Tunda kuwa ta sake ta shigo da kanta rayuwa ta ,ta wargaza min dukkan shiri na to ya rage nata sbd sai na tabbatar tayi nadamar decision din ta

Yau lahadi kwananta bakwai kenan tun ranar datamin wulakancin nan bata kara ganin ido na ba sbd dan halak ta mawa wulaqanci koya take ma oho na tabbatar taji babu dadi sbd by now tasan da ita da babu duk daya.

Banida wani aiki sosai dan haka sai ten na tashi a bacci zuwa eleven na shirya sam na gaji da cin abincin gurare gashi banson zuwa gida inci magana taje gurin Abba gashi bazan taba cin jagwalgwalon wannan yarinyar ba don karma ta fara daukan kanta a matsayin mata ta

Wai mata mtssseww

Shawara na yanke gidan ya Amina zanje inci a can zuwa twelve na kwashi mukullaina na fice

Ina zuwa nace akwai abinci tace bari a dafa maka bayan mun gaisa Zainab tace ina aunty Hanaan nace tana nan ya Amina tace kamar ya tana nan tana lafiya?

Na 'dan tab'e baki na oho nace ranta ne ya b'aci tace wa yaranta suje d'aki bayan sun tafi ta balbaleni da fad'a

"Hishaam ban gane abinda kake nufi da oho ba kana son ka shiga wutane?"

To bahaka kukeso ba na fada ina daga kafadu na kinsan ban iya k'aryaba gaskiya rabona da ita tun randa aka kaita gidan nan kuma daga haka babu abinda zan iya qarawa"

Shiru tayi nad'an lokaci tana kallo na kamar wani wanda yayi kisan kai ni kuwa na zaro waya ta na fara dannawa

Can ta nisa tace to wallahi ka gyara ko kuma in had'ka da Abba banda wulaqanci ko akuya aka d'aure da sunanka ai ya kamata kasan halin da take ciki meye amfanin aurenka datayi?

To me kikeso inyi? What do you want me to do huh"?

Wlh ka shiga hankalinka na zata kanada hankali shiyasa na qyaleku amma yanzu tunda haka kake to zansaka maka sharadi kullum kaje ka dubata sau biyu safe da dare

"Okay guard din ta zan zama kenan ko meye"?

Zan dinga yi mata waya duk ranar daka sab'a hakan zaka amsa kiran Abba wato ma kasan abinda kake ba daidai bane amma babu ruwanka ko? to yanzu inma mutuwa tayi bakasaniba kenan"?

Gabana ne ya fara faduwa ta cigaba kuma daga yau ka gama cin abinci a gidan nan kaje kaci na matarka"

"Allah ya kiyaye inci jagwalgwalon wannan yarinyar"

kuma ka tashi ka tafi yanzun...karar wayarta ne ya katse zancen ta daga da sallama

Abba ina wuni gabana ya fadi jin Abba ne kullum sai ya min waya akan wannan yarinyar maganar ya amina ce ta katsemin tunani da cewa to Abba me zai hana kaje ka duba su daga nan sai hankalinka ya kwanta kuma shima Hisham din zaiji da'di ai wuyanta ta nuna min da hannu alamun yanka ni Abba zaiyi yanzun?

Abba kayimasa wayane?

Mukullaina na d'iba na daga mata hannu na fice sai gida

A bakin kofarta na tsaya cikin rashin sanin abinyi, a raina nace me to zanyi mata,me zance mata haushi na cika dashi

A hankali na tura kofar wani sassanyan qamshi ne ya daki hancina daman gani mayen qamshi da daddare na shiga gurin sam ban lura da yadda aka qawata shi ba sai yau sai sanyin air-con da yake tashi gabadaya yanayin qamshin part d'in nata kamar aci ji nayi jiki na ya mutu murus kamar in sami guri in zauna inyi ta jin qamshin musamman ma idan ba zan ganta ba

Kamar me sand'a nake tafiya babu koda motsi a wajen mummunan faduwar gaba naji nace kardai fa ta mutu ko wani abu ne ya sami yarinyar nan na fara tafiya da sauri daidai qafar benanta naji motsi a kitchen

Kujerar dake saitin kitchen d'in naje na zauna tana tsaye a kitchen d'in da mopp a hannun ta tanata gugar kitchen sai a lokacin na tuna ba helper a gidan gashi Abba yanzu zaizo damn it

Tun daga kanta na fara kallon ta har qafar ta nayi saurin dauke idona nace shameless girl batasan wanda zaizo ba amma jibeta bum-short ne a jikinta sai blouse ta daure gefen rigar koyaya ta motsa ana ganin cikinta a fili kanta da wata hula iyaka tsakiyar kan kawai ta rufe wayarta tana aljihun wandon ta saka earphones a kunne gashinta wasu yan jeloli sun fito ta gefe da gefen fuskar ta

Sam bata san da mutum a falon ba bansan yadda akayi ba na sami kaina da qare mata kallo ban taba ganin mace a yanayi irin wannan ba sai yau nace a raina

da badan rashin tarbiyya ba ai da anyi mace a nan koda yake shedan ma zai iya qawataki don ance mace tana tahowa ne da siffar shedan kuma tana bada baya da siffar shedan

Shetan kuma na tambaya ba shedan sai dai mala'iku su qawata ta ka manta matarka ce haushin tunanin danake ne kawai ya kamani har naja to tsaki ba tareda nayi niyyar hakan ba inda hakan ya saka ta juyowa muka ha'da ido da ita kafeni tayi da idanuwanta masu cike da tambayoyi she have sexy eyes qwalla ce tafara cika a idonta nace araina ai daman yarinya a lokacin kukan ki kike ni kuwa ba raino nazo ba ballantana inyi lallashi idan kuka ya zamar miki jiki a gidan nan da kanki ma zaki dena

Kanta ta sunkuyar a qasa ganin haka yasa na dauki remote na kunna TV bayan qofa ta koma ta boye sam daina kallon gurin nayi nace a raina yau sai surukin ki ya ganki a haka zanga qarshen zama ba kaya sai misalin biyu sannan Abba ya qaraso inajin motarsa na fita da sauri amma abin mamaki kafin mu shigo da Abba harta saka abaya ta nad'e kanta tsaf ita kanta sai data gane kallon mamakin danake mata

Kayan hannun Abba na hana yaran gidan su karb'a na karb'a da kaina bayan mun shigo ya zauna sai gata da sauri ta durqusa ta gaisheshi ina mamakin irin sonda Abba yake mata dama ni yake so hakan a qasa ta zauna bayan sun gaisa ta tashi ta nufi kitchen na bita don kartayi kwab'a ruwa da lemo ta hado a tray ta d'auko ta wuceni ta fito na biyo bayanta na karb'a na ajiye na zuba masa bayan ya natsa yace in bata kayan nan ya fara mata bayani fa cewar

"Hanaan ga uniform dinki nan da duk abinda zaki buqata na makaranta

Gobe zaki fara zuwa nasan kinada tarbiyya da kamewa amman inason ki qara saboda yanzu ke matar wani ce ba'a zuwa da mota ba'a zuwa da waya makarantar duk abinda kikeso ayi miki ki tambayi mijinki gashi nan ko babu aure 'dan'uwanki ne akwai ni'ima da Amal da zainab naji an maida Anisa ma kinga akwai tarin yan uwanki acan kiyi karatu sosai kinjiko? ta gya'da kai tana kukan da na rasa dalilin sa kuma

Abba be gusheba saida yayi mana nasiha ya sanar damu haqqin mace akan mijinta ya sanar damu haqqin miji akan matarsa lallai Kam abin babbane yayi ta sa mana albarka inata amshewa cikin jin da'di ina sosa kai ita kuwa na lura abin ya shigeta sosai

Har gurin motarsa muka rakashi ta juya da sauri zata wuce nace inason magana dake "

"Bismillah tace ta wuce gaba ina bayanta muna shiga falon banjira tayi wani abu ba na fara magana.

"Kinji abinda Abba yace? shiru tayi tana kallona da alama ma haushi na take ji inda hakan ya bani qwarin gwiwa na cigaba idan kinji to ya tsaya iyaka fatar kunnuwanki karki sake ya shiga cikin kanki idan kuma bakijiba to haka nakeso dan bana son gaba kice na baki false hope

Shiru ne ya ratsa dakin ko dana fuskanci babu abinda zata ce juyawa nayi zan fice

"meyasa ka amince da auren nan?"

abinda tace kenan naji dad'in tambayar datayi domin ni mutum ne da baya son b'oye b'oye murmushi na saki nace

" the same thing da abinda yasa kika amince wato auren nan shine freedom d'ina kamar yadda yake naki kema kin gane yanzun"?

"shikenan dalilin ka na aurena?"

" Eh shikenan don haka bana son ki kira auren nan da sunan aure ki d'auka nan gidan haya ne da muka ha'da kudi muka kama ni da ke babu mai tashin wani kuma babu mai iko da wani babu kuma me takurawa wani karki ta'ba zaton wai saikin tambayeni akan duk abinda zuciyarki ta raya miki kiyi. zaki iyayin duk abinda kikeso bazai dameni ba hawaye naga tanayi banason kuka shiyasa na sake juyawa zanfice tace to in aure kake so me yasa saini?

Na juyo da sauri na d'aga kafada ta nace wannan ne kuma nima ban saniba tunda ni bance a hadani dake ba ko da wata asalima da yarinyar danake masifar so kuma banjin zan iya son wata mace bayan ita

To donme yasa baka gayaminba?cikin kuka take maganar har tana shashsheqa nace ai na baki duk satar amsa akan kice bakyason auren nan kika qi ni kuma daga bangarena ban isa ince banaso ba dan haka kada kiga laifina.

Meyasa baka aureta ba ka batamin tsarin rayuwata akan wani plan d'inka na daban mara amfani wannan ki tambayi b'angarenki kuma karki saka rai zan zama direban ki ko in zama me raino don ke din baki wuce rainoba a gurina ya fice yana wata irin dariya da zata baka haushi koda kuwa ba da kai ake dariyar ba.

HANAAN
*********
Tabbas haushin sa nakeji kuma shi koda yaushe saidai katsam ka ganshi ina tsaka da gugar kitchen na ganshi yana kallona daman shi baya kunyar kallon mutane kamar be ganni ba ni kuwa nace gidan ka tarar mamaki nake meya kawoshi out of nowhere da besan da mutum a gidan ba saiyau jinai ina neman kuka na rasa me yasa rashin damuwar sa da ni yakemin ciwo sosai b'oyewa nayi a bayan 'kofa saboda bana buqatar ya ganni a haka kuma bazan ta'ba bari yaga kuka na ba don be cancanci ya gani ba

Qarar mota naji daman bana saukowa a haka abaya ta na zura na yane gashina da mayafinta Abba ne a fili mamakin sa ya fito ganin jikina a rufe cikin qanqanin lokaci nace a raina wato qarancin shekaru yasa mutumin nan yana min kallon shashasha kenan harda wani biyoni kitchen sai a lokacin na gane abinda ya kawo shi sashena sabida Abba zaizo ne bayan Abba ya tafi banyi niyyar kulashiba sam sai yace yanada magana maganar datafi wuta zafi a tare dani

Tun lokacin da muka gama maganar nan na shiga tunanin irin rayuwar dazan tsarawa kaina don gudun wulaqanci sbd na fuskanci wata biyayya da qasqantar da kai da nuna sanin ya kamata baza su saka yaga mutunci na ba domin ya riga ya tsara hakan kuma ko me zanyi bazan ta'ba samun gurbi a zuciyar sa ba domin akwai wata a gurin yanzun na riga nasan hakan to gara ma inyi rayuwar da zatamin da'di

Akan ce wai idan kaga mamaci ya dawo tsoron sa zakaji ni kuwa gani nake da Ayya na zata dawo da zanso hakan koda kuwa fatalwar ta ce ba lallai inji tsoron ta ba musamman ma da na san ko fatalwar Ayya ba zata cutar dani ba

Haka na kwana ina saqa da warwara da addu'ar mafita me kyau daga ubangiji da dan kuka na qasa-qasa sbd rashin gata na da rashin Ayya ta.

Tun asubha da nayi sallah na zauna na fara rera karatun Qur'ani na bayan gari yayi haske na shiga kitchen na ha'da breakfast nad'an ci ka'dan uniform d'in makarantar farar t-shirt ce me dogon hannu da collar a wuyan sai palmerant d'inta ash skirt d'in ma ash a bude yake gabadaya daga qasa inda ya taho a tsuke daga sama sai farar socks da farin hijab din da ake kira da talha iyakarsa wuya sai baqin cover shoe na dade ina kallon kaina a madubi nace lallai Kam banwuce raino ba.

Fuska ta ta dan kumbura sbd kukan dana sha sbd haka na fara qaqalo murmushi sbd kar inje insha tambayoyi

Harabar gidan na fito tun bakwai da ashirin ina zaune har takwas ina kan lilo yana kadawa sannu kan hankali nayi nisa da tunani na rungume jakata kamar ance kalli sai gashi ya fito yasha ado cikin qananan kaya yayi wani masifar kyau tsanarsa ce ta kamani dana tuna yanada wadda yakeso baniba a hankali na taka kamar bana so zuwa inda yake tunda na taho yake kallona ni kuwa yanzun in yana kallona bana damun kaina daf dashi na tsaya nad'an rusuna barka da asubha hannu kawai ya dagamin hade da cewa lafiya

Na cije labena na qasa saboda haushin rashin daraja ta a gurin wanda na zaci shi yayi ra'ayin aurena da kanshi ko dana d'aga kaina sainaga yana murmushi har ana ganin hakoransa inda naji zuciya ta tana neman yaudara ta nayi saurin kautar da kaina ina dan sosa kai da yatsa na

"how childish"

Nan da nan nafara tafasa da irin rainin hankali da yake min. Nace ba zuwa nayi kayimin dariya ba lift nake da buqata saboda ban waye da gurin da zani ba kuma naga yanzun kake fita

Mamaki yayi yadda yaji maganar ta fito daga bakina a gadarance ba kamar da ba da nake lanqwasa masa harshe na da magana mafi taushi wani lokacin ma ina magana tana sarqewa

"kash yau ba yanzu zanfita ba"

yafada tareda dafe kai kamar yana magana da yar shekara uku ban tsaya wata-wata ba na juya na koma kan lilon cikin garden ina kukan rashin sanin abin yi can na tuno da buhari ciki na koma da sauri na dauki waya na kirashi ko minti goma ba'a yiba sai gashi, na kulle ko'ina ina qoqarin fita yazo fyuu ya wuceni da mota bansan ina kuka ba saida naji hawaye masu dumi sunabin kumatuna inda na ta'ba su cikin mamaki buhari ne ya miko min tissue na shige na zauna ina goge hawaye na

Muna fara tambaya a take aka kwatanta mana da yake sananniya ce banda a gurin kifin rijiya irina don bana yawo sam kusan ma babu inda ba sani da kaina.

Yau tayi da'di sosai abinda na fuskanta daya da makarantar shine babu tarbiyya kamar tsohuwar makarantar mu ga Anisa kuma harda ni'ima Allah yaso ba ajinmu daya da anisaba amma ni'ima ajinmu daya kowa abinda yaga dama yake kamar makarantun da nake gani a turai mazan sai cakumar matan suke nikuma daman can na tsani irin wannan harkar.
Muna karatunmu successfully makaranta ka'dai ke deben kewa shi kuwa sai inyi sati banganshiba sbd na bawa banza ajiyar sa nima na kanji kamar zanyi hauka wataran da son ganin sa dukda bansan me ya janyo hakan ba amma sai in kanne idan na tuna babu alkhairi a ganin nasa

Abin mamaki kullum dai yanzun yana zuwa in yaji motsina koda be ganniba saiya wuce nakan leqo inga kwalliyarsa kafin ya fita amma fa bana isarsa kallo ballantana fa magana.

Yau asabar ina gida farar shirt ce qal a jikina da bakaken stones an rubuta lucky me da duwatsun jikin ta, wuyanta qato ne sai bakin wando jeans iyakarshi gwiwata banason gashina yayi qura saboda ba kullum nake jiqashi ba musamman ranakun school hulace baqa a tsakiyar kaina kawai take nasa pin na maqaleta

Ice cream na dauko a fridge na fito falo da zummar zama kawai sai ganin mutane nayi a dan razane na kalleshi sbd i wasn't expecting anyone

ko ba'a fadaba nasan itace yarinyar da yake so saboda yanayin kallon dayake mata. Kamar ana cakamin mashi a qahon zuciyata haka nakeji kallon banza takemin na duba naga na fita komai gashi tayi sa'a dashi kuma yana gani saina tuna cewa ni'din fa ba kowa bace sai kawai na hade raina na d'aga kafadata da girata alamun tambaya cikin dariyar raini yace bakuwa na kawo miki ku gaisa daman kinsan da labarinta sbd ki tabbatar.

Zuciyata naji tanamin yaji sai na saki murmushi nace oh you are welcome zasu shigo nace wait suka tsaya suna kallona a tare takalmin d'aki na d'auko musu suka canza ba musu. Bayan sun canza suka shigo a tare kitchen na shige ina sauke numfashin dayake barazanar barin jikina kuka kawai nakeson nayi amma nayi alqawarin bazai tab'a ganiba

waishi meyasa duk lokacin dana dade ban ganshi ba ganina dashi baya zama alkhairi ya Allah ka taimaka min,

Lemuka na kawo musu ashe ya iya hira ban saniba sai yau arziqin wata.

Ban zuba musu ba shiya zuba musu saboda ban iya kinibibi ba suna sha suna hira na lura zamana bashida amfani a gurin na tashi nace to baquwa afwan akwai ayyukan dazan qarasa yanzu ki gaida gida na juya da sauri yace itama tafiya zatayi kamar ba haka taso ba amma sai tayi murmushi tace na tafi nace mungode da ziyara sai wani lokacin na rakasu har ya bita nace Dr ya juyo da sauri cikin mamakin na kira shi nace minti daya ba musu yace ina zuwa yana shigowa na dubeshi nace meye alaqata dakai dazaka kawomin baquwarka? a zaman haya fa there are some rules so karka qetara don't cross your limit after all kana da part dinka why don't you just take her there?

"What"??
"Oh yes"
"Me kike nufi?"

"kina nufin inkaita dakina?"

Me yayi saura tunda ka kawota dakin matarka

karki qara kiran kanki da matata kuma karki qaramin rashin kunya.

Yamm naji kaina yana yi nace waito meye matsayina a gurinka shiru ya danyi kafin yace you are part of my properties, yafada yana dariyar mugunta

tunda nake ban ta'ba jin rashin mutunci irin na yauba kuka ne yake qoqarin subucemin na kalleshi murya na rawa nace did you just call me your property? Am not... anyone's... property kuma na gane abinda yasa kakemin wannan abubuwan harda kawomin mace gida so kake kayimin kora da hali so for your kind information ban ta'ba sonkaba Kuma bazan tab'a sonka ba sabida baka layin irin mutanen daya kamata a soka ko baka kyautatamin dan komai ba zaka kyautata min saboda qaunar datake tsakaninka da mahaifiyata amma tunda ka manta daga yau na manta alaqar datake tsakanina da kai kuma bazaka ta'ba samun abinda kakeso ba domin bazan tab'a rabuwa dakaiba har sai na tabbatar na tarwatsa duk wani buri da kake dashi yanda ka batamin budget kaima saina tarwatsa duk burinka kuma i dare you ka fadawa Abba duk lokacin daka gaji da zama dani.

Ko ba'a fad'a ba maganganu na sun shigeshi musamman dana sako zancen mama na sbd na fuskanci har yanzun yana ganin girman ta

Cikin b'acinrai ya kamo dantsen hannu na duk biyun ya matso dani dafda fuskarshi har naji tsoro sbd ban ta'ba zaton hakan ba

yace me kika d'aukeni? zakice inkai mace d'akina cikin tsiwa nakalleshi nace yadda ka d'aukeni ko ka zata ban san irin kallon da zargin da kake wa y'an gidan mu bane???

Cikin mamaki yake kallona na fizge jikina tareda fadin karka qara tabani na wuce na barshi a tsaye cikin mamakin yadda na canza gabadaya.

Tun wannan lokacin na daina yin duk inda zamu hadu dashi sbd hakan yana karya zuciya ta musamman kuma yadda nake masa rashin kunya tunda ba halayya ta bace sam bana jin dadi duk da dai shi yake janyo hakan kuma idan ba hakan nayi masa ba sai yayi tamin abubuwa amma da zarar na datse shi sai yayi qus.

HISHAAM
**********
Hishaam yarinyar nan zarginka fa take I'm sorry to say zama fa da zargi haramun ne kuma kafi kowa sanin haka nifa ina bala'in jin tsoron yarinyar nan Hishaam karta qwacemin kai shukra ke wadannan maganganun a gefe ina tuqi zan kaita gida

Harga Allah banso shiga gonar yarinyar nan ba dondai shukra ta matsa ne kuma banason b'acin rai haushi maganar ta bani nace a qwace ni kamar yaya sai kace wani kaya

Nan dae muka canza wata hirar da zata mana dadi

Tun ranar da tamin rashin kunyar nan ban qara ganintaba wani abin mamaki dana lura dashi shine, ban tab'a ganin tana magana da daya daga ma'aikatan gidan nan ba bakuma ta fita ko'ina sannan kullum da asubha karatun Qur'an dinta ne ke tashina abarci saboda bedroom dina da nata qofa kawai ta rabasu.
'Impressive'

Yau a gida naci abincin rana bayan na gama kenan Mom ta shigo tana tsaki nace Mom what's wrong meya faru tace a abin haya na dawo wai direban bashida lafiya.

Yawwa boy dan Allah jeka d'auko min ni'ima a makaranta mana

Okay

Ba musu dukda dai banson shiga cikin yara a mota ta na tafi har qofar ajinsu tunda ba wani shamaki na tsaya ita ta fara fitowa tsayawa tayi tsaf tana kallona cike da mamakin ganina wani dan ajinsu ne ya fito bazaifi sa'antaba ya dubeni yace uncle wannan fa bata son kallo kagane

Au kallon ta nakeyi kenan?

Ni'ima ce ta fara masifa bakasan yayana bane yace ko waye shi din. Dan qaramin bakin ta ta bude tayi magana cikin nutsuwa

"fuhad ka barsu kawai"

Kamar an watsamin wuta naji inda kuma a take na fara tunanin to me ya batamin rai har hakan
haushine ya kamani na dubi ni'ima nace Mom tace inzo in d'aukeki kuma banason bata lokaci idan kika qara minute daya to zaki nemi hanyar gidan ku a qafa

Zainab ce ta fito bayan mun gaisa nace kema shiga in ajiye ki a gida tunda dai na zama driver yau

Tana tsaye a inda take y'an maza sun zagaye ta amma kamar hankalin ta baya kansu, da sauri Zainab taje tace anti Hanaan mubi uncle Hishaam mu tafi yau ma baza'a zo d'aukarmu ba yau tace

"kibishi ni zan tafi kawai"

Da sauri ta fara tafiya ta barmu a tsaye ina kallon su zainab tabi bayanta wasu y'an ajinsu suka bisu abaya suna cewa yau gorgeous ranta ya b'aci muje mu rakata daya ya karb'i jakar ta d'ayan kuma sai zuba zance yake na rasa meyasa sainaji raina yayi mumminan b'aci

Da gangan na bada musu qura yarinya qarama sai tsabar girman kai na banza da wofi kawai na wuce su da gudu sbd gurin titi ne sosai sbd a main hanya yaje ni'ima ta leqa tana musu dariya raina ya qara b'aci na take burki da qarfi tayi gaba ta buga kai jikin dashboard cikin haushi nace why don't you grow up you are so annoying

"sorry Yaya"

Ina kaita gida ban tsaya shiga gida ba gidana na wuce zan shirya inkoma aiki. D'akina na wuce nayi wanka na fito ina goge jikina sheshshekar kuka nakeji can qasa-qasa, qofar d'akina na matsa dake cikin dakinta inajin sheshshekar ta ahankali

Jikina ne yayi sanyi wani lokacin inason yi mata wasu abubuwan amma sai inrasa amfanin hakan sbd na tsani raini shiyasa bana wasa da Ni'ima ratar tayi yawa kasa fita nayi sam kamar wanda aka doka kuma aka hanashi fita dr Sadiq na yiwa magana yayi covering d'ina kwanciya nayi inajin motsinta cankuma sai shiru

Ji nayi inason ganinta yarinyar ce hartama fini ji dakanta tsaki nayi na miqe ahankali nake tafiya qofar falonta na farko na tura sainaji a kulle nace au fita tayi kenan mukullin qofar na d'auko na bude na shiga ahankali abin mamaki tana zaune a carpet tayi tagumi gashinta ya rufe fuskata da kafadunta gaba daya Masha Allah nace bansanma na fada ba gyran murya nayi ta juyo a tsorace ido ta tsareni dashi ciki mamaki da tsana gashinta ta nad'e ta dauki mayafi ta rufe ta dubeni cikeda tsiwa tace tsarin naka hayar kenan?

Narasa ma me ya kawoni can idea tazomin nace ina kallon ki kina yawo da wasu yara harkuna hada kafada ko? Meye matsalar ka da hakan?babu nace a taqaice tace to don Allah karka qara zuwa nan wlh nagaji da ganinka a rayuwata kuma duk sanda na ganka hakan baya haifar da alkhairi. Maganar ta daki zuciyata musamman da yanayin datake maganar kamar tanason tayi kuka tana tabe dan qaramin bakin ta tareda buqa qafan ta a lokaci d'aya

Nace eh amma ai kinason ganin wasu qarti ko?

"Eh din"

tafada da qarfi

Saboda qartin su suka damu dani kuma duk matsayinsu dai ban kaisu gidan wani ba ko? ba kamar waniba daya dauko wata ya kaita gidansa. Iyakacin quluwa na gama quluwa nace idan kika cigaba da yimin rashin kunya wataran zan cire bakin nan ta murguda bakin tace wannan bakin wanke hannu ka ta'ba ne nace ko kuma ka ta'ba ka wanke hannunka ba??

Tace koma dai meye yafi na budurwarka na kasa bata amsa sbd na fuskanci ta dade da fara raina ni

ta wuce ta bani guri.

Na rasa me yasa idan tana abubuwa kamar wanda ake riqewa sai in rasa me yake hanani yin komai saidai kawai in kalle ta Koda yake su ai daman y'an gidan su basuda kunya da itace ma kamar me kunyar kafin halin ta ya bayyana.

Comment