TSINTACCIYAR MAGE part 53/54

_*TSINTACCIYAR MAGE.....*_🌷
  _a true love story_


_*BY~AUFANA*_ _wattpad@Aufana8183_


® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚


  _*Page 53/54*_


_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_


Saikusan 9pm sannan tadawo gida tana dawowa kawai tawuce d'akinta tatufe, wanka tai sannan tai sallah tai shirin bacci tai kwanciyarta,,....


Washe gari ma bata fitoba sai kusan 9am sannan tai wanka tashirya tafito, d'akin hajiya taje tamata barka da safiya sannan taje d'akin Abbu a can ta tadda mai martaba da sarki nanta durk'usa takwashi gaisuwa cikin tsintsar ladabi suka amsa mata tareda sakamata albarka sannan tafito,,....


Tana fitowa saitai kicib'is da MUJAHID zaishigo, dasauri taja da baya tai tsuru tana kallonsa, murmushi yasakarmata sannan yai tsaye ya rungume hannayensa yana kallonta, murmushi itama tasakarmasa sannan ta duk'arda kanta tace masa "barka da safiya mr man" cikin murmushi yace "barka dai amaryata fatan kintashi cikin lafiya" tace "Alhmdllh" gyara tsayuwarsa yai yakalleta yace "lafiya baki fito break ba d'azu kowa yafito kekad'aice" d'an sosa kanta tai kamar mara gaskiya sannan tace "umm....um bacci ne yad'aukeni wallahi bayan nagama sallah" yai murmushi,,,.....


Ammar ne da musty suka shigo da gudu cikin uniforms d'insu, dasauri musty yarik'e hanun MUJAHID yanafadin "yeee narigaka wallahi nine number one" tsaye ammar yai yakwabe fuskarsa kamar zaiyi kuka, dasauri MUJAHID yarik'o hanunsa yana fadin "a,a my Lil bro karkayi kuka mana kai namijine kazama jarumi kaima watarana kamatsa sosai kacinyesa kazama number one kajiko" murmushi ammar yai yace "dagaskiya brother me nima zan iya cinye musty nazama number one kullum fa musty shike na 'daya a school a komaima shike na 'daya"  yai maganar cikin yanayin kuka,  MUJAHID yai murmushi yace "sosai ma kuwa zaka iya amma saika daina kuka kadinga jajircewa sannan zaka iya zama nmbr one kaima kadaina kuka akan yacinyeka kaima kayi karatu kayi kokari kai na d'aya, yanzudai meya maidaku gida ba school kukajeba" musty ne yai saurin cewa "ammar ne yamanta littafensa na homework kuma auntyn mu duka take sosai shine muka dawo ya dauka" itadai MUFIDA kallonsu kawai take tana dariya, MUJAHID yace "ok oya to kuje ku d'akko kuwuce school kuma kuyi karatu sosai" suka ce "toh" sannan suka wuce da gudu,,,....


Mayarda dubansa yai gun MUFIDA datai tsaye tana kallonsu tana murmushi, shima murmushin yai saitacemasa "wannan rigimar tasu ta tinaman abunda yafaru abaya daga cikin labarina" murmushi kawai baice komaiba saita juya tawuce abunta tana share y'an kwallanda suka zubomata,,,.....


    Kimanin kwanansu MUJAHID biyar a k'asar Nigeria sannan suka tattara suka koma k'asar BAGDAAZ yana kewar abar k'aunarsa haka itama tana kewarsa sosai,,,.....


MUFIDA tacigaba da fita aikinta saidai batajin dad'in aikin yinsa kawai take gashi yanzu ayyuka sunmata yawa kusan kullum suna kan hanyar k'asashe daban daban domin kulla alak'a da wasu companonin daban hakan yasa yanzu batada lokacin kanta bare kuma nawani wani lokacin ma dole saita kashe wayarta saboda kar adameta da kira,,,....


              *****  *****


Rayuwa tacigaba da gudana cikin farinciki da walwala tini aka raba gadon Alhj Doctor Ahmad Shitu dukiyar MUFIDA kuma aka damk'amata abarta, a ranar wuni tai kuka saboda abun yatinamata da rayuwarta ta baya yanda dady ke nuna tsintsar kulawarsa a gareta yake bata gata da jindadi tamkar yarsa tacikinsa daya haifa, tai kuka sosai kamar ranta zai fita saida tagaji tabama kanta hak'uri,,,.....


Munira tadawo itama ta kammala degree d'inta MUFIDA tashiryamata walima had'addiya sannan tabata kyauta mai tsoka ta musamman, a ranar kuwa saida sukai kuka sosai saboda tinawa da mahaifinsu, tinda munira tadawo suka koma gidansu kasancewar akwai security's kuma dik hadiman gidan sunanan donhaka suka koma acan,,,....


Anfara shirye shiryen biki a dika gidajen biyu nan gida Nigeria dakuma can BAGDAAZ, tini Amira ta'iso nan suka hadu sukafara shirye shiryen,, bak'i sunfara isowa na nesa dana kusa tini gida yafara cika da bak'i Aunty maryam taiso yayar hamma faruk itace ta d'auki nauyin dikwani gyara da zaayiwa amarya, akwatayya uku tacikowa MUFIDA da English were's had'addu masu d'aukan hankali had'eda kayan bacci kala kala ita MUFIDA abunma kunya yakebata dan ko kallon kayan bataiba saida Amira tad'akko tabud'e sannan suka gani tanata dariya wai ita wallahi bazata iya saka waennan kayan ba Amira tace "hmm ganinku muke b'arayin barkono dakanki zaki kira kice asake kawomakisu idan akwai" dariya tai takaiwa Amira dukan wasa,,,.....


Yau kwana hud'u kacal yarage afara gudanarda bikin, mahaifiyar MUFIDA tazo tareda k'annen MUFIDA da mijinta da y'an uwanta guda bakwai maza da mata da yara y'ammata uku, hakan bak'aramin dad'i yayiwasu abbu ba nantake aka taryesu cikin fara'a aka kaisu masauki, ranarda sukazo takira MUFIDA a sirrance sukai magana sannan tadamk'ata kud'i naira dubu d'ari shida da wasu kayan mata na sha, godiya tamata sosai sannan takarbi kudin tawuce,,,".....


Tini Aunty maryam tafara gyaran MUFIDA gyara nakwarai wankan dilka da kurkur,  wankan lalle, tiraren tsuguno, girki da ruwan bagaruwa,  tsalki da ruwan lalle da bagaruwa, romuwar kazar hausa da gundarin namanta, haka tasakata agaba tana gyaranta aikuwa cikin y'an kwanaki MUFIDA tamurje tak'ara kyau tsintsar kyanta yabayyana a fili kyakkyawar surarta tak'ara fitowa tai fari tass fatarta sai sentsi take tana shining tai laushi kamar ta jinjiri sabon haihuwa, ita kanta tasan tasauya jin kanta take kamar baita ba,,,....


Yau kwana 'daya kacal yarage afara gudanarda shagalin danhaka aka d'aukesu akawuce dasu gun gyaran suma da lalle da gyaran jiki, saida akamasu lalle sannan akamasu saloon abun gwanin birgewa abunka da fararan fata saisuka zama tamkar larabawan asali,,,....


Yau itace ranarda zaafara event 1 wato kamu, around 3pm suna zaune a gidan aunty maryam na G.R.A wanda ke kusa da gidansu MUFIDA gidan dadynta saiga nusaiba kawarsu MUFIDA ta ukunsu driver yakawota nan, farinciki agunsu baamagana nanfa suka rungume juna cikin tsintsar kewar junansu, saida suka gaisa sannan suka shiga ciki akafara firar yaushe rabo,,....


4pm dot akafara gudanarda kamun anan gidan aunty maryam d'in, amarya tai kyau bakad'anba kamar ka d'auketa ka tsere tai kyau tamkar y'ar tsana tasha make-up kayanta white color material zane da riga dinkin yoruba anmata nad'i da d'an kwalinta, sai kusan 7pm sannan aka gama gudanarda kamun kowa ya watse,,,....


Washe gari su MUJAHID suka iso shi da abokanansa da Rayyan kasancewar anan ne za'ad'ura auren kuma washe gari ne, hakan yasa dole suzo a yau d'in,suna isowa suka had'e dasu Amira nanfa sukaita barkwanci abokanan ango da kawayen amarya abun gwanin birgewa, 10pm motocin su ango sukazo d'aukan amarya da kawayenta izuwa diner, a katafaren holl d'innan ROYAL za'agudanarda diner d'in, wata tsadaddiyar wedding gown ce amarya tasaka blue and white color shikuma angonta tsadaddiyar shadda ce yasaka gizna white color riga da wando da babbar riga wacca tasha aikin hanu blue color hakama hularsa blue and white color ce, sunyi kyau matuka amarya tasha make-up sukuma su Amira wani material ne suka saka suma blue and white color sunsha make-up, hakama su Rayyan shadda ce sukasaka white color tasha aiki blue color amma su ba manyan rigina Rayyan ne kadai yasakata, suna isowa aka budewa amarya da ango suka fito hanunsu a sakale dana juna MUJAHID saifaman wasan hakora yake yana dariya, Rayyan da amira ne suka shiga a gaba sannan sukuma sukabi bayansu sannan saran kawayen nasu da abokanan ango, atare suka shiga cikin holl d'in suna fara shiga nanfa akafara basu flasher ana d'aukan su hotuna abun gwanin birgewa, saida suka isa gunda aka tanadar domin ango da amarya suka zauna sannan sukuma sukaje suka zauna,,,....


Bayan anyi hotuna sannan aka yanka cake daganan akafara shagali, saida akabama amarya da ango fili sukad'an taka sannan k'awayen amarya da abokanan ango suka shigo sukafara liki suna taka rawa suma, daganan kuma kowa yadinga shigowa yana taka rawa yana liki, sai kusan 2am sannan aka gama diner d'in kowa yawatse,,"...


Saida suka sauke amarya da kawayenta gidan aunty maryam sannan sukuma suka wuce,,....


Washe garine za'adaura aure kuma za'ayi Arabian day saidai acan BAGDAAZ ne za'ayi arabian day d'in,,,, washe gari tin 8am suka shirya ita da kawayenta sukabi jirgin 10am sukawuce BAGDAAZ, 12pm dot dubban mutane suka shaida d'aurin auren MUJAHID ABDUL-SAMAD da MUFIDA AHMAD SHITU, d'aurin aurenda yasami halartar manyan mutane ciki kuwa hadda sarkin k'asar BAGDAAZ da manyan y'an boko da shahararru kasaitattun y'an kasuwa da shuwagabannin gomnati, bayan angama d'aurin auren MUJAHID yashirya walima hakama su abbu ana gama walimar su MUJAHID suka hau jirgi suka wuce BAGDAAZ,,,....


           *BAGDAAZ*


Wasu shahararrun matane MUJAHID yanema suka saka MUFIDA agaba da gyara tamkar ba'ataba mata wani gyaraba haka suka dinga gyaranta ita abun yabata mamaki sosai wai MUJAHID ne kuma yaturosu yace sugyaramasa amaryarsa tsab kai maza dai basuda kunya, bayan sungama ne sannan suka shiga yimata make-up na zuwa arabian day d'in, wata rigace suka sakamata gown ce pink color har k'asa da mayafinta sukamata rolling dashi sannan suka sakamata takalma hils silver color, bayan sungama saisuka kirasa suka shaidamasa sunkammala, saikusan 4pm sannan sukazo suka d'aukesu izuwa gunda za'ayi,,...


Wani katafaren holl ne na MUJAHID wanda yake 'daya daga cikin abunda ya mallaka, angyarasa sosai yasha kwalliya da flower's kala kala da bolom bolom kowa ya hallara amarya da angonta kawai ake jira danhaka suna isowa akafara gudanarda event d'in, dik wanda zaka gani acikin wajen to zaka gansa sanye da jallabiya mata kuma abaya jallabiya na mata kuma dikansu arab's ne saisu Amira ne kad'ai ba arab's ba,,,....


Yan nasihohi ne akai akan zaman aure daga bisani akai walima akaci akasha akai al'adun larabawa sannan aka rarraba y'an kayan walima 6pm kowa ya watse, daga nan kai tsaye gidan mahaifin MUFIDA wato tajudeen aka wuce da'ita da kawayenta, sunjima sosai acan saida tai wankan lalle tashirya tsab sannan aka kaita gun mahaifinta, nasihohi yamata masu ratsa zuciya da gangar jiki akan zaman aure da biyayya ga miji, banda kuka ba abunda MUFIDA keyi saboda tinawa da dadyn ta datai ranarda za'akaita gidan hamma faruk shima irin waennan nasihohin yamata,,,.....


Yajima sosai yana jan hankalinta daga bisani aka wuce da'ita masarauta, acan ma sakata sukai a gaba da nasihohi masu ratsa zuciya sai kuka take tana kara tinawa da dadynta a zuciyarta tanata masa adduoi,, 8pm dot motoci sukazo suka d'auki amarya da kawayenta da sauran mutane izuwa gidan mijinta Biryama MUJAHID...............




#/Vote
#/Share
#/Comment


'''AUFANA for life '''
  *I.W.A*🖋

Comment