ABDUL JALAL 85

.๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน ๐ŸŒน


_ABDUL JALAL (2020)_


_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)


PART 2
_PAGE 3๏ธโƒฃ2๏ธโƒฃ85


Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]



_MY FIRST NOVEL _


Jalila tace "Yasalam, Nana kiname Ilham zata shigo har cikin gidan nan ta daukarmin abu natane? Meya kai hannunta kayanmu harta daukarmin abu"


"Jalila Al'qurani fa ba Novel bane ko littafin hausa da zan kamata da kokawa in karba, gyaran daki nakemana tashigo ta ganshi ta dauka"


"Nana kingama dani dakika bari ta tafi dashi, amma tunda tace idan na dawo na je karba ki gayamata ta saurari dawowarta wa, tasan karona da ita ba dadi, zanzo in karba idan bata bayar dan Allah ba zata bayar dan dole, karma kikuma tada maganar tabaki zan dawo in karba, banda Jahilace me zatayi da Al'qurani metasani aciki? Inma tasani bashida amfani a gurinta ai"


"To nidai Allah yabaki hakuri, ni bayan haka wasu maganganu tazomin dasu dasam ban gane inda ta dosa ba?"


"Kamar yaya?" Jalila ta fada a kagauce


"Nikam Baby meye hadinki da Jalal ne?"


"Wane irin tambaya ne wannan Nana?"


"Jalila inkinga rashin mutuncin da Ilham ta dingayi a dakinmu sekinsha mamaki, tana gayamin wai na hada kai da ke zaki kwace mata Jalal, wai taga abunda ban ganiba, Kina son Jalal ne, Naja tazo suka hadu sukayi tayi, ni abun yabani mamaki iya sanina ko shiri bakwayi dashi amma maganganunta sun ban mamaki "


Jalila tayi ajiyar zuciya tace


"Nana kyale ta aikinyi ne bata dashi, kinsan tun asalina yarinyar nan batayi min ba, shiyasa take neman masifa, nime zanyi da wani Jalal, ai Jalal se ita makakkiya itama din ba Auren ta zeyiba, ki manta da ita zan dawo ai daidai nake da ita ai"


Nana tace "Hmm Jalila kenan, inaji kaman kina boyemin wani abune, amma inba rami meyakawo rami? Shikenan dai sekin dawo din, ki gaida min Hanan dan Allah ๐Ÿ™"
Nana ta kashe wayarta, Jalila ta kalli Hanan a salube,
"me Nana take nufi?" dan daga mata gira Hanan tayi tace
"Queen kenan, naga kin damu da abunda Ilham tayi, amma keda bakyasonsa meyasa kike son abunda yafito daga hannunsa haka har kikejin babu dadi?"


"Hanan bansan mezan gaya miki ki yadda dani ba wallahi, Hanan Al'qurani abune me girma, sannan inason sanin meye Jalal ya ajiye tsawon lokaci ni banganiba, sannan muddin ina raye Wallahi sena nunawa Ilham iyakar ta"


"to meye na wannan tada jijiyoyin wuya haka easy queen i know you can do it, amma meye next plan dinki akan Jalal, kina ganin tafiyarsa Dubai akwai Alkhairi kuwa?"


"To yatafi uwar Dubai mana, daga nan yatafi bangon duniya idan yanaso? Ke nagama abunda zan iya akansa kowa tasa ta fishsheshi, dama yace ina takura masa kinga se yaje yayi abunda ya gadama, nima takaina nake, yatafi bayan duniyama yaje ya bude gidan giya in yanaso"


takarasa fadin haka tana kokarin kwanciya
Hanan tace
"karya kike tawajena, nasan halinki kaf Jalila yanzu kina jin wani abu ze sameshi zaki kuma tashin hankalinki, kya gama zagaye zagayenki ne"
Banza Jalila tai mata ta ja bargo ta shige, Hanan tai murmushi itama ta kwanta.


Jawwad yaje kiran da Mummy take masa, amma ya lurada wani kallon banza da Ilham take masa bebi takanta ba ya durkusa ya gaida Mummy dake zaune a palour,
Har kasa ya durkusa suka gaisa, Mummy tace


"yawwa Jawwad dama nace kazone saboda Jalal, inason ganinsa amma nasan nidashi bazezo kiran danake masa ba, dan Allah Jawwad ka dinga yimasa fada, sati me zuwa daddynsa zezo akwai maganar danake so muyi nida shi da babansa, dan Allah idan daddynsa ya dawo zanmaka magana inaso ka kawomin shi "
Jawwad yace
"insha Allah Mummy zan masa magana, acigaba da hakuri ana masa Addu'a Insha Allah komai ze wuce, Alhamdilillah yanzu yafara rage wasu abubuwan"


"Hakane Allah yasa hakan nima ina masa addu'a"
Yatashi yai sallama yafita, Ilham tayi tsaki tace "Nifa Mummy gani nake wannaan Jawwad din ke kara ziga Jalal yake wani rashin mutuncin yake kara kina"
"Kinga nidai ba wannan ba, kokarina kawai inga abunda na shirya ya tabatta akan auren nan naku, idan kika matsa kika nuna bakyason Jawwad kinsan baze taba aurenkiba ko? Dan haka kishiga hankalinki"
Ilham ta zumbura baki ta tashi tabar palourn.


Zaman bauchi ya karbi Jalila, tayi kalau da ita, kusan koda yaushe tana tareda Anty fiddo kokuma gurin inna, susha hira taci dariya, gashi cousins din Hanan suma 'yan shaftane mazansu da matansu, haka ake zuwa a cika babban palourn gidan aita wasa da dariya, samarin gidan da yawansu suna suna son Jalila amma fafur Hanan tace, ai Jalila tanada miji. akwai wani cousin din Hanan yusuf akayi bikinsa, komai da Jalila akeyi, kaikace 'yar gidance dama can sunsanta, sunajin tsoron yusuf sosai saboda baya wasa ma sosai, anan gurin babban abokin ango ya like yace shi nan duniya Jalila yakeso, Yusuf yaji dadin hakan, dan haka yace "Aitunda daddy yace da Hanan da Jalila duk' ya'yan sane, shima da Jalila da Hanan duk kannensa ne, ya yaba da halin Jalila dantafi Hanan nutsuwa"


Bayan biki yusuf yasamu daddyn Hanan, yagaya masa Abokinsa Ahmad yana rikon 'yar baba
Daddy yai murmushi yace


"indai' yar baba ce inta amince sannan kun cika ka'idojinmu ai semu duba inkun cancanta abaku semu baku"
Yusuf yace


"daddy kenan indai ana sanmu ai zamucika dukkan sharudanka" daga nan sukayi ta hira daddy agaban Mummy akayi tace


"Amma danayi murna, dan Ahmad mutumin kirki ne zataji dadin zama dashi, amma ina tunanin yadda zata zauna da matar Ahmad, kasan 'yar taka bata da hakuri' ya'yannak ban san wadda tafi wata hakuri ba"
Daddy yace "Ai indai tana sonshi lafiya kalau zasu zauna, inmuka koma zanyiwa Abbanta maganar, indai basuyiwa wani Alkawari ba, Zanbawa Ahmad"
Yusuf yaita godiya kaman shi za'a bawa.


Daga Jalila har Hanan basu san me akeyiba Yauma, an taru a palour ana hira da daddare Daddy yake cewa abashi list din sunayen wanda ze samawa aiki, Jalila ba karamin birgeta family din nan suke ba, kansu a hade yake haka aka gama hira aka watse.
Jalila kullum tana tareda Inna, sannan Mummy Hanan duk ta dena mata wannan wulakanci datake mata abaya.


Jalila suna chatting da suleiman yake gaya mata, an tabattar da Alhaji Kabiru yana saida makamai da kwayoyi shida Jeje, ranar litinin za'a kaisu kotu, Jalila ba karamin farinciki tayi ba, taitayi masa godiya. Ta zauna tayi shiru tayi wani tunani, amma bata gayawa Hanan ba tasan damunta zatayi da tsokana dan haka tabar abun a ranta


Da safe Jalila bayan sungama breakfast taje tasamu Mummyn Hanan tace "Mummy dan Allah kan daddy ya fita inason inganshi"
Mummy tace "to shikenan zan masa magana" Hanan tace "queen me zakicewa daddy ne? Ina fatan bawata matsala?"
"Ba wata matsala inason inganshiine"
"to shikenan"
Mummy taiwa Jalila iso, taje palourn daddy , ta shiga suka gaisa yanata tsokanarta tana murmushi, se bayan sun gaisa tace
"babana gurinka nazo kamin wata Alfarma"
"Ina jinki 'yar Baba fadi komene? Insha Allah in zan iya sena miki shi"
Jalila ta kwashi kusan Awa guda a gurin daddy sannan ta fito, ko Hanan bata gayawa Abunda ta tattauna da daddy ba.


Har yanzu Jalal baya walwala sosai, daddynsa yadawo Nigeria, yakan shiga cikin gida gurin daddynsa, amma babu ruwansa da Mummy balle wata Ilham, Iyakar Jalal dakinsa, sedai wani lokacin yakan fito amma baya nisa sosai, Jawwad ne ke takuramasa yadan fita dashi suzaga gari, Jalal yadena zuwa club amma yana shaye shayensa a dakinsa be denaba.


Hannah duk yadda zatayi taga Jalal abu ya gagara, dan haka ta yankewa kanta shawara ta karshe, ta shirya tsaf ta tafi gidansu Jalal, Jalal na cikin dakinsa a kwance besan me akeba, daddy yana gaggawa ze fita da yamma motar Hanna tai parking a kofar gidan, ta fito daga motar da wata irin shiga da bata kamaci dan musulmi ba, da sauri takaraso gaban daddy tace "barka da yamma"
Yace mata "yawwa barka" ya dauke kansa yana kokarin bude motarsa tace "Amma dan Allah Jalal fa?" seda gaban daddy ya fadi, kaddai ace Jalal yafara neman matane ya dake yace mata "lafiya me Jalal din yayi miki?"
"meyema bemin ba? Amma dan Allah yana cikine gurinsa nazo, inason ganinsa" kaidajin yadda Hannah ke magana kasan babu Alamun tarbiyya a tareda ita daddy yace
"Meye alakarki dashi dakike nemansa, baki bani amsa ba"
"Akwai alaka me girma tsakanina da Jalal, sanin Alakar bata da amfani a gareka, babu abunda sanin Alakar ze kara maka banda bacin rai da tashin hankali, dan haka bekamata ayi tone tone ba, amma ina neman Alfarmar ka dan girman Allah kasaka baki Danka ya Aureni, hakan ne kadai hanyar tsira da mutuncina"
Mummunar faduwar gabace takama daddy, hasashensa yazama gaskiya kenan, yanzu lalacewar ta Jalal harta kai ga fara neman mata Innalillahi wa inna ilaihi raji un juyawa daddy yayi da sauri ya rike kansa ya shige cikin gida yana hada hanya.
Hannah kam murmushi tayi tace "koda banganka ba Jalal, nayi abunda nasan dole ka nemeni, na fuskanci bakajin rarrashi kafiye taurin kai, gara in fito maka a Hannah ta.
Ilham na palour tana harabar gidan tana waya daddy yazo ya wuce rike da kansa, mamakine yakamata, yanzun nan fa yake sauri ze fita to shida waye, sauri tayi ta nufi gate ta leka, amma taga anja mota batagane waye ba.
Gida ta dawo taje tagayawa Mummy, da sauri Mummy ta fito ta nufi part dinsa yana zaune ya dafe kai akan kujera, zama tayi kusada shi tace
"meyasameka hakane? Habibi lafiya kuwa yanzufa kake cikin walwala kafita meke damunka ne?"
Dagowa yayi idonsa jawur yace "Khadija Jalal"
"meyasami Jalal din? Bashida lafiya ne?"
"ba wannan ba, ina kyautata zaton Jalal yafara neman matan banza" dan zaro ido tayi "Kamarya ya'akayi kasan haka? Kodayake ba abun mamaki bane ba, tunda duk wanda yake shan giya koya kwana a club ba abun mamaki bane amma gaskiya bana zaton Jalal yana neman mata amma"
"Enough!!! Baze yuwu ba khadija, iya sanina ฤana ba manemin mata bane ba, ban san ya'akayi haka zata faruba, kinga yarinyar datazo gurinsa yanzu kuwa? Kinsan metace min ne? No baze yuwuba dole in dau mataki, Zina bala'i ce, dole inyiwa tufkar hanci"


Ilham dake labe a kofar dakin sedata kusa rusa ihu, da gudu ta tafi dakinta ta rufe kofa tana sintiri, nashiga uku idan Dagaske Jalal yafara neman mata ina na kama, menene makomata? Kan bala'i hakan na nufin lalacewar komai fa? Amma wacece tazo gurin nasa? Ina baze yuwu ba, idan har Jalal yafara neman mata bazamu samu komai ba gaba daya shirinmu ze lalace ne, dole inje inga umma a yau din nan jakarta ta dauka ta zuba kudi tayi waje da sauri tafita ta tari napep ta nufi gidansu.


A sukwane Ilham taje gidansu, ta tarar da mamanta a tsakar gida tana tankade, "Umma akwai matsala ajiye tankaden nan ki tashi"
A sukwane tace "ke lafiya kike wannan rawar jikin?"
"nikam ki ajiye tankaden nan kitaso akwai matsala"
Jan hannun mamanta tayi sukayi daki ta zauna a gefen gado tace "Umma akwai gagarumar matsala, mahaifin Jalal yace yafara neman mata, wai wata yarinya tazo neman Jalal, be fadi me tace masa ba, amma yace yana zargin yafara neman mata, idan haka ta faru mu menene makomarmu?"
"ki kwantar da hankalinki kitashi kikoma tun kafin su gane wani abu, ki bar komai a hannuna gobe da kaina zanje gidan malam, ya bincikamin tsawon shekaru mutumin nan yana mana aiki, bamu taba samun matsala ba dan haka bana tunanin za'a samu wannan matsalar "
" gara dai kije da gaggawa kar asamu matsalar wannan karon, dan ina cikin matukar tashin hankali "
" bakomai ki tashi ki tafi"
Sukayi sallama Ilham ta taho.


Gaba daya hankalin daddy yagama tashi, yarasa nutsuwa gaba daya, yana murna yana ganin Jalal yafara rage wasu abubuwan amma kawai ace wannan mummunan tashin hankali da abun kunya na gabato family dinsu. Ganin duk ya tashi hankalinsa yasa Mummy tasame shi tace
"Hayatee wannan damuwar ba iyace mafita ba, nasha gaya maka abaya Yakamata ayiwa Jalal Aure, Namiji ne me cikakkiyar lafiya dole ya bukaci abokiyar rayuwa, amma wakake tunanin zebawa Jalal Auren 'yarsa a wannan halin nasa, shiyasa nace tunda Ilham ta nuna tana sonshi a haka kima' yar uwassa ce, kayadda a hada Auren nan, shine rufin Asirin mu, kila ma kaga ya dena abunda yake"
Daddy yai ajiyar zuciya yace "bakin Auren Ilham da Jalal nake ba, ina gudun abunda ze biyo baya ne, kinsan halinsa inbayason abu, yace baya son yarinyar nan, tunda yace bayaso ko anyi Auren nan wahala zata sha"
"Haba Hayatee kafison yadakko maka magana atukuna, a wajene yake cewa bayaso, da anyi abun zakaji shiru sun zauna lafiya amma kayi tunani, ina tunanin ayiwa Jalal Aure shine mafita, tunda banajin ma yanada wata wadda yakeso giyarsa ce kawai ta dameshi, inaga yiwa Jalal Aure shine mafita"
"to shikenan zanga abunda Yakamata nayi, Amma hankalina tashi sosai".


Bayan sallar magariba Jawwad yasa Jalal agaba da mita
"Gaskiya Jalal bana son wannan zaman gidan da kakeyi kadena walwala, kadena farinciki kullum a daki, bana son hakan, inaga zan duba mana wani business mufara kadena wannan zaman, dan haka zanyi tunani business zamu fara"
Jalal yai murmushi yace "Dama ina son yimaka magana, Daddy yacemin yasamomaka aiki amma kaki yadda katafi, karka damu dani Jawwad ka karbi aikinka ka tafi senafi kowa murna, Saura kuma muzo musha bikinka da Hanan, ko angon Hanan?"


Ajiyar zuciya Jawwad yayi yace "Jalal nina rasa mekemin dadi ma, Maama ta matsamin akan Auren Naja, kullum yarinyar nan setayi abunda zatajamin fada a gurin Maama, narasa yadda zanyi da ita"
"Kaine bakayi maganinta ba"
"Kamar yaya kenan?"
"Keje kasamu Abba ka gayamasa yanema maka Auren Hanan mana"
"Taya Jalal? Jalila tana sona idan na Auri Hanan ban kyauta ba Jalal"
"kana maganar kana son ta tana sonka amma meye makomarta agurin mahaifiyarka da danginta?"
Jawwad yai ajiyar zuciya yace
"Kasan wani abu makuwa?"
"A'a seka fada"
"Hanan tace min wai soyayyar 'yan uwantaka ce tsakanina da Jalila, Akwai wani a zuciyar Jalila, amma kana ganin hakan ze iya yuwa?"
Jalal ya dan kalli Jawwad yace
"Hmm Maybe, nidai fatana kaje ka karbi aikin nan kawai da daddy yasamo maka in bahakaba nida kaine"
Jawwad yai murmushi yace "Jalal kenan sedai mutafi tare".


Abbaa ya kira Jawwad dakinsa, gashi ga Mummy Jawwad ya shiga ya zauna yana fatan Allah yasa ba wani laifi yayi ba.
Abba yace
"Yayana na kaina, Maamanka tazomin da wani batu, shine nace yakamata ingaya maka kafin in aiwatar"
Jawwad yace
"to Abba na ina jinka"
"Yawwa Jawwad, Maamanka tace tanason hada Aurenka da Kanwarka Naja, kuma nan da sati biyu takeso akai kudin Auren, sannan ka karbi aikin da'aka sama maka, in anyi Auren se ku tafi can tare"
Duk wata jijiya ta jikin Jawwad seda ta dan tsaya na wucin gadi, gaba daya jikinsa yayi shock, cikin dakiya yace
"To Abbana, Allah ya tabattar mana da Abunda yafi Alkhairi gaba daya"
Maama tayi murmushi tace
"in ankai kudin banason asa fiye da wata shida"
Jawwad yace "to Maama Allah ya temakemu"
Abba yace "ina fatan dai ba'a matsa maka ba, inkana da magana ka fito kayi"
Jawwad yace "A'a Abba babu wata damuwa"
"to shikenan Allah yamaka Albarka"


Haka Jawwad yafito daga dakin jiki ba kwari ya tafi dakinsa ya kwanta


Jalal yayi mamaki jin shiru Jawwad bezo ba yau, dan haka ya mike domin yaduba Jawwad, daddy ya kirashi a waya yace yana son ganinsa a cikin gida.
Cikin gidan ya nufa, ya nufi palourn daddy amma yana zuwa ya tarar da
Daddy, Mummy, dakuma Ilham turus yayi ya tsaya yana kallonsu daya bayan daya, yasan akwai wata kulalliya


Ina yinku ABDUL JALAL group irin sosai din nan fa ๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜ inajin dadin Comments dinku, kuna Comments kana karamin kaimi typing duk bayan kwana biyu, kuna bari ina lalaci posting duk sati ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ


Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ๐Ÿ–Š๏ธ
What's app only 07063065680.

Comment