BAYAN WUYA part 19

🌷🌷 *BAYAN WUYA*....... 🌷🌷
                      🌷


*(it torchs the herts of the readers based on true life story)*


*writing - by*
*ameenart Umar fana (AUFANA)*


Β Β  *DEDICATED TO - hussaina uthman abubakar (UMMUN MEENAL)*


_this page it's for you my lovely sister BALKISU (MRS ADAM) inajin dadin comments naki sosai Ina godiya Mara a dadi Allah ya bar zumunci ya barmu atare Allah ya saka da alkhairi kasani fa Ana mugun tare irin a makalkale dinnan fa πŸ’– I HERT YOU OVER AND OVER LOVE YOU SO SO MUCH πŸ’–_


Β  *PAGE 90-95*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Cikin tsananin razana tayi tsaye ganin baba ya shigo yana kallonta karasawa yayi cikin falon yana masu wani mugun kallo ganin mama Sarah tsaye yasa ya Kalle ta cikin kakkausar murya yace mata miya kawoku gidana ki tattara kubarman gida na idan dai Har ba tsohon naku bane bata iya cemasa komaiba saima kwallar da take zubarwa *INTISAR* ce ta taso cikin kuka Mai tsanani ta durkusa a gaban baba tace don Allah baba kayi hakuri ka yafewa abbana da mamana don Allah kayi hakuri ubangiji ma mukan masa laifi mu rokeshi Kuma ya yafemana kayi hakuri baba don Allah kuka take sosai tanaΒ  rokonsa surayya ma tasowa tayi tana kuka ta kama INTI duniya tayiwa baba zafi kasa tsayuwa yayi da kafafunsa zama yayi Kan kujera ya dafe kansa da duka hannayensa yana zubarda kwallah Mai zafi yana fadin na cuci kaina na cuci dana na biyewa rudar shaidan da zugar zuciya na raba dana da yanuwansa SADIQ ka yafeman ka gafarceni Dana kuka yake sosai hjy ce tashigo tana sharar kwallah tace dama irin wannan Rana nake jira tazo wlh da ace abubakar lalacewa yayi to tabbas kaine Mai babban laifi ba irin hakurin da bamu baka ba nida yarannan nayi kuka nayi kuka amma kaki hakura shi wanda ma kakeyi akansa ya juya maka baya yarsa kuwa tana can tayi aurenta harda Yaya Kuma iyayenta suna kula da ita sosai amma Kai ka kori danka Kahana iyalinsa sanin dangin su yanzu gashi Ranar danasi da batada rana Kuma bata da amfani MAJID ne yatashi tsaye yace yanzu dai hjy komai ya wuce ayafewa juna Abba kuwa ubangiji yamasa rahama yagafarta masa ya Kai haske a kabarin sa ameen suka amsa Yaya Hussain yaje kusa da baba yace baba kayafewa abbanmu murmushin karfin Hali yayi yace Dan Nan nayafewa SADIQ dina Kuma zanci gaba da yimasa adduah Har karshen rayuwata Alhmdlh MAJID yafada Allah shine abun godiya baba ga Yan jikokinka nan wannan shine babba ya nuna Hussain Sai wannan *INTISAR* saikuma autarsu BADEEYAH koh surayya murmushi yayi yace masha Allah Allah ya Raya Akan sunnah ameen


Hussain ya kalli baba yace toh Kai Dan tsoho baka tambayi wannan ba murmushi yayi yace ai nasan sa ba *ABDUL-MAJID* bane dangidan ALHAJI MUKHTAR dariya Hussain yayi yace eh shine ai duk yashigo Garin saiyazo ya gaidamu dariya Hussain yayi ya kalli MAJID yace nafada ne Shima dariya yayi yace bansaniba tini INTI tagano Inda suka dosa don haka tabar falon tayi wajen su mama coz su suna cikin gidan jaira Yaya Hussain yace toh shine KESON *INTISAR* cewar Hussain aa Kai masha Allah kace tuwona maina zaayi kenan toh Allah ya gwadamuna lkc ameen suka amsa


Β  ******Β  ******Β  ******


Batareda wani bata lkc ba hjy ta kirasu IBRAHIM tasanar dasu komai ba karamin jin dadi sukayi ba cikin kankanin lkc IBRAHIM YAYAN ABUBAKAR ABBANSU INTI ya iso tareda iyalinsa haka ma ASMA'U itama tazo da nata yayan su AHMAD autan hjy Shima yazo dayake yayi aure harda Yaya biyu maza nanda Nan gida yacika da yanuwa da abokan arziki abun gwanin ban shaawa su INTI dadi sukeji yau gasu cikin Yan uwansu Kuma Sai Nan Nan ake dasu coz su *INTISAR* kyawawa ne duk gidan mahaifiyarsu suka dauko tamkar LARABAWA musamman MA ita *INTISAR* yanzu girma yazo mata komai na jikinta ya bayyana musamman kirjinta cike yake tab dana shanu 😍 mama yau cike take da farinciki Ina ma ace abubakar yana raye yagani da idonsa Kash mutuwa bakimin adalciba yar karamar kwallah ta share da sauri coz batason yaranta su gani zasuyi ta tambayarta meya faru shiyasa bata barin suganta idan tana kukan tinawa da mijinta anan suka wuni Ranar cikin Yan uwansu cikin familyn su Sai nishadi suke


Sai dare wajen 10:30PM Sannan MAJID yazo ya daukesu suka wuce gida cikin jin nice Kamar karsu tafi saura kwana daya Yaya Hussain ya wuce school atare zasu wuce da MAJID da daren yaje gidansu hjy ya sanardasu kudi baba ya bashi masu yawa godiya yayi masa Sannan ya masu sallama ya wuce


Tin 90:00am suka kama hanya su INTI na kewarsu sosai Yaya Hussain yafara karatunsa cikin jin dadi coz baya neman komai karatune kawai agaban sa su INTI kuwa kusan Bayan kwana biyu duk suna gidansu hjy wani lkc ma Har kwana suke acan abata karsu da ZAINAB kuwa Sai kara kaimi take saboda bazata taba mantawa da zainab ba ta taimaketa sosai a rayuwa


Ginin gidansu *INTISAR* ya kammala coz aiki ake sosai baba alhj ma yabada kudi asaka domin aikin yayi sauri su INTI Ana waya da mutan Abuja alhmdlh yanzu Kam su *INTISAR* rayuwa suke Mai cike da jin dadi da farinciki Abu daya suke tinawa suyi kuka ABBANSU wanda sukayi alkawarin yimasa adduah Har karshen rayuwarsu baba alhj da kansa yasa driver ya Kai su INTI gidan ABBANSU Ibrahim kwanan su biyu acan Sannan sukaje gidan gwaggonsu asma'u acan ma saida suka kwana Sannan suka dawo


Β  Β  Abba Ibrahim jira yake exam dinsu INTI ta fito coz so yake tacigaba da karatu ya canzawa surayya school from government to private school wacca yanzu ss2 take godiya su INTI keyiwa ubangiji daya sauya masu rayuwa daga wuya zuwa dadi


Hakane *INTISAR* dama *BAYAN WUYA SAI DADI*haka Allah yake lamarinsa


*ABUJA CITY*
MAJID ya koma bakin aikinsa amma da zuwansa yashaidawa dady komai gameda soyayyar sa da INTISAR dady yaji dadi sosai Kuma ya saka masa albarka dakuma fatan alkhairi............




Kubiyoni πŸƒπŸΌβ€β™€πŸƒπŸΌβ€β™€


  AUFANA for life 😘😘😍🌷🌷🌷

Comment